Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakatar da ayyukan asusun kula da kanan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF a arewa maso gabashin Najeriya sai nan gaba.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta zargi hukumar agajin da horarwa da kuma tura 'yan leken asirin Boko Haram.
Batun dakatar da ayyukan UNICEF din dai ya zo da mamaki ga ita kanta hukumar, kuma ta shaida wa manema labarai cewa ta na tantance bayanan da zargin ya kunsa.
Sanarwar dai ta fito ne daga bangaren Operation Lafiya Dole, wani shirin rundunar na dakile Boko Haram.
Ta zargi hukumar da horar da mutane don yi wa ayyukan rundunar zagon kasa a kokarinsu na yaki da Boko Haram.
Rundunar sojin dai ta yi ikirarin cewa an yi wa 'yan leken asirin horon ne ran 12 da 13 ga Disamba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Miliyoyin mutane a Arewa maso gabashin Najeriya ne Boko Haram ta daidaita, kuma da yawansu sun dogara ne da agaji domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
A rahotonta na baya bayan nan, UNICEF ta yi kiyasin cewa kananan yara miliyan 4.5 ne ke cikin tsaka mai wuya a Najeriya..
___________________________
Rundunar Sojin Najeriya ta ja wa UNICEF kunne
Rundunar sojin Najeriya ta soke matakin dakatar da ayyukan asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF a arewa maso gabashin kasar kamar yadda ta sanar da farko.
Rundunar dai ta zargi UNICEF da zagon-kasa ga kokarin da sojoji ke yi na yaki da Boko Haram ta hanyar horarwa da kuma tura 'yan leken asirin Boko Haram.
Sai dai a yanzu kusan ana iya cewa rundunar ta yi amai ta lashe, bayan wani taron gaggawa da ta ce ta gudanar da wakilan UNICEF.
Wata sanawar dauke da sa hannu mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanar Onyema Nwachukwu, ta ce a lokacin tattaunawar, sun shaida wa hukumar ta agaji kar ta kuskura ta yi kafar ungulu ga ayyukan sojin a arewa maso gabashin kasar.
Haka nan kuma an umarci wakilan UNICEF da su ringa sanar da mahukunta a duk lokacin da za su bai wa sabbin ma'aikatansu horo.
Da fari dai, rundunar ta fitar da sanarwar da ke zargin UNICEF da yin zagon-kasa a yakin da ake da Boko Haram ta hanyar yada labaran karya ko marasa sahihanci.
Wannan ba shi ne karon farko da rundunar ke kwan-gaba kwan-baya a kan matakin da suke dauka kan UNICEF ba.
Ko a wata Afrilu, ta bayyana wasu ma'aikatan hukumar uku da ta ce ba a bukatar aikinsu a kasar, sakamakon zargin cin zarafi ta hanyar lalata da aka kwarmata a kan sojojin Najeriya.
Sai dai daga baya rundunar ta sauya shawara tare da janye kalamanta.
_________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 news Update;
Wakilinmu;
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST
Tags:
Labaran Duniya