'Yan Boko Haram sun kai hari garin Gudumbali na jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun kai hari garin Gudumbali na jihar.
Rahotannin sun ce sojoji sun dakile harin, amma an samu asarar rayuka daga dukkan bangarorin.

Wasu mazauna garin na Gudumbali sun ce mayakan sun yi gaba da kayan abinci da kuma makaman soji.


Kawo yanzu dai, rundunar sojin Najeriyar ba ta ce komai ba game da harin.
A watan Yuni ne gwamnatin Najeriyar ta yi kira ga dubban mutanen da suka gudu daga garin na Gudumbali sakamakon hare-haren Boko Haram da su koma gidajensu.
     ____________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update;
Wakilinmu
   👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST

Sunday 16/12/2018

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post