kasashen Yamma abokan ittifakin Saudiyya ne suka tirsasa saudiyyar yada Wahabiyanci a duniya

"Daman Turai ce ta tirsasa mu yada Wahabiyanci a duniya
Yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman ya bayyana cewa, kasashen Yamma abokan ittifakin Saudiyya ne suka tirsasa su yada Wahabiyanci a duniya da zummar ganin bayan Tarayyar Soviet a lokacin yakin Cold War.

Yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman ya bayyana cewa, kasashen Yamma abokan ittifakin Saudiyya ne suka tirsasa su yada Wahabiyanci a duniya da zummar ganin bayan Tarayyar Soviet a lokacin yakin Cold War.


Bin Salman ya furta wannan kalamin a yayin wata ganawa da yayi da manema labaran jaridar The Washington Post ta Amurka, a yayin da ya kai ziyara wannan kasar,

“Kawayen Saudiyya na yammacin duniya ne suka Tirsasa masarautarmu  yada wahabiyanci, gina makarantun Islamiyya da masallatu, a tsakiyar karni na 20 don hana tarayyar Soviet samun gindin zama a kasashen Musulmai.Makudan bilyoyin dalolin da muka zuba don yada wannan akidar sun fito ne daga kungiyoyi, hukumomi da ma’aikatu masu zaman kansu da ke kasarmu. Sarakunan Saudiyya da suka gabata sun aikata babban kuskure.Yanzu lokaci ne ya kamata a ce mun gyara kura-kuranmu”.

Jaridar Al watan ta tabbatar da sahihancin wannan bayanin na Yarima.

      _______________________________
Ma'asumiya Nigerian News Update
Wakikinmu .

Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post