Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewa ba ta kai farmaki gidan ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku bubakar sai dai ta kai wannan samame ne don ta yi awan gaba da ‘ya’yan tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji.
EFCC ta bayyana cewa hukumar ta dade tana fakon su a dalilin zargin yin sama da fadi da kudaden gwamnati da suka yi a lokacin da mahaifin su ke gwamnan.
” A binciken da muka yi mun gano cewa ‘ya’yan Orji na biyan Naira miliyan 13 duk shekara na haya.
A yau Litinin ne PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin yadda Hukumar EFCC ta kai samame a wani gida wanda ‘ya’yan Atiku Abubakar biyu ke zaune a ciki a makon da ta gabata.
A cikin ginin, akwai gidan Chiemeka Orji, dan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji. An ce shi ma sai da EFCC suka binciki gidan na sa.
Amma dai majiyar mu ta ce an kai farmakin ne gadan-gadan kai tsaye a gidan ‘ya’yan Atiku da ke Maitama a ranar Asabar, kwana daya kacal bayan da aka yi zargin cewa EFCC sun kulle asusun banki na dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Peter Obi.
Sai dai kuma EFCC da ICPC duk sun musanta zargin sun kulle asusun na ajiyar Obi.
Jiya Lahadi Paul Ibe, wanda shi ne kakakin yada labarai na iyalin Atiku, ya ce EFCC ta kai wa ‘ya’yan Atiku guda biyu, Aliyu da Mustapha farmakin kwakwaf a gidajen na su, amma ta kasa samun duk wani abin da zai iya sa a kama su da wani laifi.
A lokacin da EFCC ta kai harin, Aliyu da Mustapha duk ba su gidan. Amma dai an tafi da wadansu da ke zaune a cikin ginin, wadanda su ma aka shiga aka kwashi wasu kaya aka yi gaba tare da su a ofishin EFCC.
Cikin wadanda aka tafi da su, har da Chiemaka da kanin sa, dukkan su ‘ya’yan Sanata Orji. Chiemeka ya ce an tafi da su ofishin EFCC kuma an yi awon gaba da motocin su biyu.
“Lokacin da jami’an EFCC suka dirar mana a ranar Asabar, sun tambaye mu ina ne bangaren ‘ya’yan Atiku su ke? Muka ce musu ba za mu nuna muku ba, saboda dukkan su ba ma su kasar nan.
“Sai EFCC suka ce mana su na da rahoton cewa an kimshe tulin daloli a bangaren da Aliyu da Mustapaha, ‘ya’yan Atiku suke. Wai su ne suka zo su kwato. Sai suka kutsa da karfi cikin bangaren na su, amma ba su samu komai da zai iya nuna cewa ana wata harkalla a cikin gidan ba.”Inji wata majiya.
Majiyar mu ta ce EFCC ta saki Chiemeka da kanin sa, amma an rike motocin su.
Kakakin EFCC ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba ya da masaniyar an kai wa gidan Atiku farmaki, amma dai ana binciken ‘ya’yan Orji ne dangane da yadda aka tafiyar da lalitar jihar Abia, a lokacin mulkin mahaifin su, tsakanin 2007 zuwa 2015.