-Kasar Saudiyya ta yi mirsisi da bukatar kasar Turkiyya na gabatar ma ta da wadanda ake zargi da hannu a kisan Dan jarida.

Kayi shere domin wasu sugani su amfana

- Ministan harkokin wajen kasar Adel al-Jubeir ya ce ba za su mika 'yan kasarsu ba
- Ya soki yadda gwamnatin Turkiyya ke bada bayanai akan lamarin
Kasar Saudiyya ta yi mirsisi da bukatar kasar Turkiyya na gabatar ma ta da wadanda ke da hannu a kisan shahararren dan jarida Jamal Khashoggi.
Ministan harkokin wajen kasar Adel al-Jubeir ya ce ba za su mika 'yan kasarsu ba.
A makon da ya gabata ne shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyep Erdogan ya bukaci Saudiyya da ta gurfanar da wadanda ake zargi da kisan dan jaridan bayan kotun turkiyya ta bayar da damar kamo su.
Saudiyya ta ki mika wadanda ake zargi da kashe Khashoggi
Saudiyya ta ki mika wadanda ake zargi da kashe Khashoggi
Ana dai na tuhumar mutane 11 da kisan dan jaridan, a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santanbul.
Wadanda Turkiyya ke so a mika mata sun hada da Saud al-Qahtani da Ahmad al-Asiri manyan na hannun damar Yarima mai jiran gado wato Muhammad bin Salman wadanda Turkiyya ke zargi da hannu da a kisan dan jaridan.
Mista Jubeir ya soki gwamnatin Turkiyya kan yadda ta ke bada bayanai, tare da dagewa kan cewa lallai sai an gabatar mata da dukkan shaidun da za su tabbatar da zargin cewa Yariman Saudiyya na da hannu a kisan.
A baya dai mun ji cewa bayan yawan korafe-korafe daga malamai da masu fada a ji, boye ko a fili, Sarki Salman na duba yiwuwar sauke dan nasa daga matsayin mai jiran gado, musamman bayan alamu sun nuna ya san da kisan da aka yi wa Jamal.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post