MANZON ALLAH (S) YANA JIN KOWANE HARSHE,KUMA YANA IYA RUBUTU DA KOWANE HARSHE!

-SAYYID ZAKZAKY(H).


To, sai ya zama suma wadansu ba'adin musulmi had suna ikirarin, harma wai da yabo cewa; wai shima annabin bai iya rubutu da karatu ba! 'Wa'iyazubillahi !.' Na wata ruwaya da aka samu daga cikin jikokinsa ya ce: Allah ya tsine musu, ya za su ce  manzon Allah bai iya rubutu da karatu ba? Manzon Allah yana jin kowane harshe yanayin rubutu da kowane harshe. To amma sai sukace; wai bai iya yin rubutu da karatu ba. Sai suna kokarin su nuns shi amatsayin wani 'aadin' mutum.

     Sannan su kuma makiya (na waje), suka nuns cewa; ai shi ma kamar da karfin tsiyane ya kafa daula. Wanda akanje gari ne a ba su zabi tsakanin alkur'ani da takobi su zabi daya. Saboda haka shahsiyyar Annabi (gida da waje) an nemi atozarta ta. Makiyan gida wadanda suka kafa daula dasunan addininsa, suka ga kuma baza su bi tafarkinsa ba, Sai yazama suna kokarin su maishe shi wata kama. Kamar kowane abu da sarki yakeso ya yi, Sai ya sa ayi mass hadisi cewa, annabi ya yi wannan abin. Ta haka nan zaku ga hadisin da aka  ce; wai manzon Allah (s) yana tsere da matansa . wannan sunnar da ba mu ganin wani liman ko wani sarki ya yi amarya suna tsere ba!

      Ko limamin kauye ne aka gan shi yana dannawa aguje da shi da amaryarsa jama'ar garin za su ce; wannan ba a nan garin za ka yi limanci ba,je ka wani wuri,jeka garin lalatattu kayi musu limanci! Amma sun rubuta a cikin littafi suka ce ya inganta! Wai manzon Allah yana tsere da matarsa. Wai Sai ainihin Sai yana tsere mata,amma   wai da ya yi teba Sai kuma ta tsere masa. Ka ga wato shi basaraken gargajiya wanda ya kafa mulki yana son ya yi wasanni,to kuma yana bukatar ya sami hadisi.

Kamar yadda yazo cewa; wani sarki Ba'abbase,alkalin alkalai,shine babban Malami a lokacin, Babban malamin fada(gwamnati),Sai ya shiga wurin sa ya same shi a dakin wanka yana wasa da Tattabaru. To, bai tsammaci alkalin alkalai zai shigo a dai dai wannan lokacin ba,yana wasanninsa(ya shiga ciki yana wasanninsa)da Tattabaru,sai ya ganshi ya shigo,sai ya ce; gafarta Malam,me aka ruwaito dangane da wasa da Tattabaru? Sai ya ce ;Na'am, 'an wane 'an wane, kala, wa kana Rasulillah (S) yal'abuhu' (ko 'sallallahu alaihi wasallam') 'kana yal'abu bil Hammama.'Wato wai Manzon Allah (S) ya kasance yana wasa da Tattabaru. To, shi da kan shi sarkin Musulmin ya yi shiru,daga baya sai yace;duk a kashe Tattabaru,tunda sun janyo an yi wa Annabi Karya.f

TARE DA WAKILIN (M.N.N.U) AUWAL M TUKUR.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post