HARIN DA JAMI'AN TSARO SUKA KAWO JIYA A KADUNA HATTA MUTANEN GARI BASU KYALE BA.

Kayi Click domin karantawa, kayi sphere domin wasu su Amfana


🇳🇬 *Ma'asumiya Nigeria News Update tare 


Jiya 15/12/2018,  Mabiya Akidar Shi'a a Nigeria Almajiran Shaikh Zakzaky(h), na Kaduna. Suka fita muzaharar cika shekaru 3 da waki'ar zariya, lokacin da aka kashe musu yan uwa da rushe musu muhallan karatu da makarantu da kama masu shugaban nasu,


Bayan fara 'Muzaharar' da sukeyi na wani Dan lokaci, sai ga gamayyar jami'an tsaron 'yan sanda, suna zuwa kawai suka fara bude wuta tare da (tear gas), a dai dai shatale talen Kano road' yayin da  mabiyan akidar Shi'ar ke kokarin rufe muzaharar.

Janyewar da Mabiyan..sukayi ya sanya jami'an tsaron suka koma kan *Mutanen gari* suka sanya musu (barkonun tsohuwa), babu labarin samun rauni ko kamu daga bangaren Mabiya Akidar Shi'ar ko mutanen gari.

Zamu bibiyi musabbabin kai wannan hari da jmai'an tsaro sukayi sai kuci gaba da bibiyarmu an an gaba.

-Ammar Ummar Udawa
         16/12/2018.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post