ALLAH BAYA MANTAWA DA ABUNDA AZZALUMAI SUKE AIKATAWA

__________BAHASI AKAN ZALUNCI 3__________

“Kada ka tsammaci Allah mai mancewa ne game da abinda azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna za su fiffito.” (Surar Ibrahim: 42)
Abinda ke kai kololuwar bayyana munin zalunci da kore shi ya zo a maganganun Amirul Muminin Aliyu dan Abi Talib (A.S.) kamar maganarsa, shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga maganarsa a khutuba ta 219 a Nahjul Balagha.

“Wallahi idan da za a ba niSammai bakwai da kuma abinda ke karkashin falaki-falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa in kwace mata Sha’irin da ta jawo ba zan aikata ba.”‘

Wannan shi ne matukar abinda zai iya surantawa a kan kame kai daga Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan konon Sha’iri koda kuwa an ba shi Sammai bakwai to yaya halin wanda ke yin dumu-dumu da jinin rnusulmi, yana handame dukiyoyin Jama’a, yana tozarta mutuncinsu da karimcinsu? yaya za a auna tsakaninsa da cikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayin zai kasance a fikihunsa (A.S.)? wannan shi ne irin ladabin da ubangiji ya yarda da shi wanda addini yake bukatarsa daga kowane mutum.

E ,lalle zalunci na daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta don haka ne yake da matsayci na farko a hadisai da addu’o’in ahlul baiti (AS) wajan zarginsa da kuma kore mabiyansu daga gare shi .

wannan ita ce siyasarsu (AS) kuma a kanta salon rayuwarsu yake har ma dangane da wanda ke ketare haddinsu yake wa matsayinsu hawan kawara .

_______________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update,
Wakilinmu;
      👇🏽
Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post