WANI YANKI NA JAWABIN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) DA YAYI A GARIN LAFIYAR BARE-BARI A SHEKARUN BAYA.

Ka danna link dinnan domin karantawa, Kayi shere domin wasu su Amfana, Kayi Comment domin Tambaya ko Akasin haka.


Daga wakilin ma'asumiya Nigeria News updates::Muhammad Sadis zaria

"Saboda haka idan akaje lahira ga chiyaman Na lokal gwamment ga gwamnan jaha ga shugaban kasa duk sunci amana Akazo da sarqoqi kana tsammanin duk sarqoqin iri daya ne?,

In kaga wani sarqan shi yafi yawa kasan menene ya faru Babban mutum ne babba ne saboda haka dole ne manya saida manyan sarqoqi,

Bance muku duk Wanda ya rike wannan mukaman zaisha sarqoqi ba Amma in yaci amana. Dun yazo a hadisi cewa kowani shugaba in yataso gobe qiyama yana fitowa Aqabarinsa za'a daure shi da mari sai adalcinsa ne zai kwanceshi Sai anyi hisabi ance shi adali ne sannan za'a kwance shi in ba haka ba,

Amma sauran mutane zasu fito ba sarqa Amma shi da sarqa zai fito yana fitowa charaf za'a daura mashi sarqa sai anyi hukumci koda mai adalci ne sai andaure shi da sarqa tukunna sai anyi hukunci ance yayi adalci sannan akwance sarqan,
To kungani kenan kunga duk lokacin da akace kana da mukami akwai dawainiya akanka Tambayoyinka kuma zaifi yawa ,

To ba babban mukamin da yafi kowani mukami. mukamin mukamai shine ayika kai musulmi ne mukamin musulumci ace kai musulmi ne yafi kowani mukami"

Daga wakilinmu::MUHAMMAD SADIS ZARIA.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post