MAULUDIN MANZON RAHAMA (S.A.W.W) YA KAYATAR YAU A GARIN KUMASI-GHANA.

Kayi Clicking din wannan shafin da shere domin wasu su amfana.


Daga; Ma'asumiya Nig. News Update.


Mauludin wannan shaikarar ta 2018 shine karo na 74th da aka gudanar yau 12 ga watan Rabi'ul-Auwal, a cikin garin Aboabu, dake cikin Kumasi a kasar Ghana. Wannan sunna ce ta babban Malamin Dariqar Tijjaniyya ‘Shaikh Ahmad Babal-Wa'iz’ wanda yaka saba gudanarwa tun lokacin rayuwarsa, bayan rasuwarsa kuma dalibai da iyalinsa suka ci gaba da tafiyantar da wannan sunna tasa ta raya ranar haihuwar Manzon Allah(s), wanda na wannan shaikarar ya kasance karo na 74th tun daga faruwarsa zuwa yanzu.

Mauludin Manzon Allah wanda Shaikh Ahmad Babal-Wa'iz ya assasa babban Mauludi ne, wanda zuwa yanzu ana qidayasa daga cikin sahun farko na manyan Maulududdukan da ake gabatarwa a duk fadin Kumasi da kewayenta. Al'amarin ya samu habbaka, ta yadda manyan mutane, kamar Sarakuna, Malamai, 'Yan siyasa da dukkanin Masoya Manzon Rahma suke halarta na cikin gida Ghana, da wajen kasa irinsu Nigeria, Benin, Togo, Burkinafaso, Mali, Niger da sauran Kasashe.

Alhamdulillah! Cikin ikon Allah kamar yadda aka saba, na wannan shaikarar ma an gabatar dashi cikin nasarar farawa da kammalawa cikin Aminci, baya ga jawabin Malamai dangane da Matsayi na Manzon Allah, da wayar da kai akan falalan Mauludi, tare da Gabatar da Tarihi na Manzon Allah tun gabanin haihuwarsa har zuwa ranar Shahadarsa.

Daga karshe kuma aka raba walima ta gangan jiki (abin ci da abin sha). Kowa yayi asuwaki da soyayyun namun dabbobi, duk sabida Annabi(s). Bayan gabatar da walima kuma aka sallami 'yan uwa. Muna sa ran kowamawar kowa da kowa gida cikin Aminci, Insha Allah.

Taken Taron: ‘MANZON ALLAH ANNABIN SHIRIYA DA RAHAMA GA DUKKANIN HALITTU’.

- Wakilinmu; Abbakar Ibraheem Kudan.
 Tuesday , 20/11/2018.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post