BA ABUNDA KE BUSAR DA ZUCIYA FIYE DA KISAN KAI

Yi shere domin wasu sugani su amfana

Inji jagoran gaskiya [Sayyid Zakzaky]


""Ko ka taba ganin qabarin wani waliyyin Allah, aka ce wannan da mugu
ne, fajiri, fasiqi yana ta cutar mutane, yana yanka mutane, yana shan jini,
shi ne ya zama wannan waliyyin? Bai taba aukuwa ba. To yaushe muke
fatan cewa wadannan azzluman, fasiqai fajirai, tsinannu, la’anannu
wadanda zukatansu suka bubbushe. Don Shaidan ya sawwala masu abin
da yake busar da zuciya. Ba abin da ke busar da zuciya fiye da kisan kai.
Don haka za ka ga Shaidanu kullum suna ma mutanensu wahayin su yi
kisan kai ne domin sun san shi ke busar da zuciya.
Allah Ta’ala yana cewa “Wa kazalika zayyanna likasirin minal
mushrikina qatla auladihim shuraka’uhum liyurduhum waliyalbisu
alaihim dinahum.” Duk shedana za ka ga an sa da kisan kai. Domin da
zarar mutum ya yi kisan kai shi kenan zuciyarsa sai ta bushe. To irin
wannan kisan kan ma sai a sa wanda lazim zai sa zuciyar ta qeqashe.
Kamar a ce jariri ne za a yanka a gasa naman a ci. Ko a tatse jinin a sha.
Lallai ni na san wani ya yi Shugaban qasar nan yana nan kuma da
ransa. Wannan dan garinsu ya gaya mani kuma ya sani ne sosai. Ya hau
kan wani dutse, shi ya san dutsen da jariri ya yanka ya gasa ya cinye
kakakaf ya sauko. Mutumin da ya yi irin wannan aiki ba abin da bai zai
iya ba, saboda zuciyarsa ta gama bushewa.
Wadannan masu busassun zukata, wai sune ake fata wai za su
gyaru, su gyara. In ka lura da kyau, mutanen nan ba sa tunanin kowa,
hatta yasu-yasu ba sa tunanin kansu. In ka ga waninsu ya yi wa wani
wani abu, ya yi domin amfanin abin ya koma ga qashin kansa ne, kowa
yana ma qashin kansa ne, ba wanda ke son wani ko a tsakanin su. In ka
ga wani ya yi wani abu, ko a ce ya yi taimako, to ya yi ne saboda
wannan abin zai sami amfaninsa a nan gaba. In ya duba ya ga ba
amfanin da zai samu ba zai yi ba, saboda ba zai taba yi saboda Allah ba,

ba zai taba yi don ranar lahira ba don bai san wadannan ba. Ba zai taba
yi kuma don tausayi ba don ba shi da ita. Ba shi da tausayi din, zuciyarsa
ta riga ta qeqashe. Ballantana wasu da ’ya’yansu ma suke tsafi, wasu da
matansu. Wai sune muke sa tsammani, macuta za su zo su zama sun
gyaru sai su gyara al’umma.

👇🏽----------------------👇🏽
*Ma'asumiya Nigeria🇳🇬 News Update, [filin jagoran gaskiya]*
*Wakilinmu:*👇🏽

Mahadi Tukur Almizan



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post