Takaitaccen Tarihin Gwagwarmayar; ‘Malama MaJeedah Abubakar daga inda muka tsaya.
Kashi na Biyu [ ll ]
Daga Shafin [M.N.N.U=MA'ASUMIYA]
Bayan Iyayena sun sami masaniya akan halinda nake ciki na zama ‘Yar Shi'a tare da fara Soyayyah da Shugaban Makarantar Fudiyyah ta Unguwar mu, kawai sai halinsu yayi matukar tashi, suka same ni suka tabbatar min da cewa sun ji dukkanin abinda ke faruwa, sannan suka bani dama ta k'arke akan tun wuri na kwance duk wata alaqa dake tsakanina da Shi'a ta zahiri da ta badini.
Barazanar Iyayena batayi tasiri a kaina ba, dukda kuwa ban fuskanci matsi sosai a gurin Mahaifiyata ba, ita kullum shawara take bani akan na bar wannan aqida tunda Mahaifina ya nuna baya so, a sakamakon zigi da yake samu daga wasu daga cikin 'yan uwansa da kuma mutanen gari. Amma da ace ta Mahaifiyatace da an bani ‘yanci an barni nayi abinda nake ganin shine dai-dai a rayuwata.
Amma ina! Mahaifiyina da sauran ‘Yan uwansa suka kafe akan ra'ayin na rabu da Shi'a, Nima na nuna turjiyata a kan ra'ayina, har a akai matakin da an hanani fita ko ina, maganar ci gaba da karatuna ya tsaya. Rayuwa ta fara canja min. Na shiga halin kunci na rayuwa kwarai da gaske fiye da yadda nayi tsammani.
Takura da halin matsi ya sanya na yanke shawarar cewa na hakura da karatun da nake da shaukin yi, yanzu kawai na yanke shawarar ayi min aure, sai mahaifina ya amince da hakan, amma bisa sharadin sai dai na kawo wani wanda ba dan Shi'a ba a matsayin wanda zan aura. Amma ni kuma naki ji da bin sharadin daya gindaya min. Haka muyita gwgwarmaya har mu kai ga wani mataki.
Na fuskanci jarabawowi da daman gaske daga Mahaifina tare da wasu daga cikin ‘Yan uwansa, matakin daya hada da Duka, Zagi, tsangwama, da dukkanin wani nau'i na takurawa. Na kasance tamkar wata marainiya mara galihu a gidan mu, rayuwa ta canja min, na shiga cikin halin kunci da tausayi, ya zamana nayi sallama da dukkanin farin ciki, na kulla abota da damuwa da bakin ciki a rayuwata.
Hauwa'un da take itace mafi Soyuwa a wajen Mahaifinta, amma yanzu ya kasance itace wacce yafi Qi da tsangwama a duk cikin 'Ya'yansa. Hauwa'un daya zamana a koda yaushe mahaifinta yana burin ya ganta a kusa da shi, amma yanzu abin saiya canja babu wacce mahaifinta ke nisanta da rashin son kallon fuskarta kamar ta. Allah sarki HAUWA'U.
Da tura ta kai bango Mahaifina ya fahimci cewa lallai koda matakin kisa zai dauka a kaina ba zan canja ra'ayina ba, kawai sai ya yanke shawarar cewa zai aura min koma waye. “Ba dan Shi'a ba, koma waye zan aura miki, amma bisa sharadin cewa...” - Cewar Mahaifina.
Wane Sharadi Mahaifina ya gindaya min kafin ya amince ya aura min wanda nake so, tare da barni da ra'ayina na Shi'anci ?
Mu hadu a kashi na Uku, domin jin yadda al’amarin ya kasance.
Daga shafin Ma'asumiya Nigeria News Updates.
Rubutawa: Abbakar Ibraheem Kudan.