Danna nan domin karantawa kayi shere domin wasu su Amfana
Daga Shafin Ma'asumiya Nigerian News Update
Tare da Wakilinmu Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
Idan ka kula sosai da irin kirar da aka yiwa wayoyin salula da a kai musu lakani da “smart Phone’, za ka fuskanci cewa an yi su ne da ummar saukaka mana rayuwa.
Sai dai da yawa a cikin mu, muna rike ta ne kawai ba tare da sanin sirrikan ta ba ko kuma ilahirin abubuwan mamakin da za’a iya yi da ita.
Gani ga yadda ake cire makudan kudi a saye su, mujallar Al’ummata ta zakulo muku wasu daga cikin wadannan sirrika, domin ko banza kuci kudin ku:
1. A lokutan nan da ka manta password din ka ko kuma zanen bude wayarka, tsaya ba kuka zaka yi ba. Ka san cewa za ka iya bude wayar ka ta hanyar tura sakon text daga wata wayar daban? Haka yake.
Ci gaba da bin Shafin Ma'asumiya, nan gaba zamu kawo muku bayani dalla dalla yadda za ku cimma hakan.
forgot-android-unlock-pattern_05_11_201
________
2. Za ka iya saka wayar ka tayi duk abin da kake so ba tare da kayi amfani da hannun ka ba. Muryar ka kawai ta wadatar.
Zaka iya yin kira, ka tura sakon text, ka shiga yanar gizo, ka tambayi wayarka hasashen yanayi na yau, da sauran su, duk ba tare da ka yi amfani da hannun ka ba.
___voice___
3. An taba maka formatting wayarka kayi kwana 3 kana kunci? Toh za ka iya tabbatar da hakan bata kara faruwa ba ta hanyar amfani da ma’ajiya da ke yanar gizo da ake kira ‘cloud storage’ a turance.
Zaka iya ajiye komai ba hotuna ba kawai kuma ba za su taba bata ba. Ko canja waya ka yi, dauko su kawai za ka yi. Ba a nan abun ya tsaya ba, zaka iya ganin ajiyar taka a koda yaushe ta wasu na’urorin daban.
_____cloud____
4. Toh dalibai ga naku. Ina wannan matsalar lissafin da ke saku cizon yatsa? Rubuta shi kawai za ku yi a kan fuskar wayarku ta dankaro muku amsa.
__,_,maths____
5. A lokacin da kake jin kasalar tashi ka je ka kunna ko kashe wutar dakin ka, za fa ka iya yin hakan ta wayar ka. Hmmm, Abin dadi na kusa.
____lights____
6. Chanza wayarka kayi kana neman hanya mafi sauki da zaka mayarda abubuwan ta kan sabuwar, zaka iya yin hakan ba tare da kayi amfani da komfuta, igiyar USB ko network ba
____CLONEit____
7. Shin ka san zaka iya kara girman ma’ajiyar RAM ta wayar ka? Idan 4gb ne zaka iya kara shi zuwa 8gb, zaka kuma iya kara 8gb zuwa 16gb da sauran su.
_____RAM_extended-w628____
8. Abin da yafi batar da wayarka ban haushi shi ne sanin cewa komai naka na kan wayar ya fada hannun wani. Shin kasan cewa zaka iya goge (wiping) wayar taka da ta bata yadda babu wanda zai gano sirrinka?
____lost phone____
9. A lokutan nan da kake bukatar kayi scanning din wata takarda amma babu internet cafe a kusa, albishirin ka, za ka iya yin scanning din da wayar ka fa.
___document scanner___
10. Ka san lokutan nan da alarm din ka zai yi kara amma baka shirya tashi ba, kuma wayar bata daidai inda hannun ka zai iya kaiwa? Toh ga albishir, zaka iya yiwa wayar magana ta yi tsit.
A sashen mu na kimiyya da fasaha, zamu na dauko wadannan abubuwa guda 10 daya bayan daya muna muku bayani dalla dalla yadda a ke yi.
Dafatan ka mallaki Application dinmu na shafinmu a wayarka domin samun sabbin Ayyukanmu, idan bakada shi kayi mana magana ta WhatsApp ta wannan number 08149993999 domin muturo ma. Ko kamana magana ta shafinmu na *Ma'asumiya Nigerian News Update* kai tsaye.
Daga Wakilinmu Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
Tags:
Yanar gizo
you are doing well
ReplyDelete