Ku latsanan domin katantawa kuma kuyi shere domin wasu su gani su Amfana.
Ma'asumiyya Nigeria News Updates tare da Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999
KASHI NA FARKO
_Ayatullahi Ja'afar Subhani
Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
Hadin Kai Sirrin Cin Nasara Hadin kai mabudin cin nasara ne ga al'ummu a kan matsaloli daban-daban da kuma wajen ci gabansu, kai baki daya ma duniya tana tafiya ne a kan ka'ida da asasi na hadin kai. Misali :-
Kananan koramu da suke haduwa a wuri guda su ne suke haifar da babban kogi, ta yadda su kuma koguna su shayar da tekuna manya-manya, haka nan digo-digon ruwa suke haifar da katuwar matattar ruwa ta yadda suke kasancewa masu karfi har su rika samar da wutar lantarki, sannan su shayar da manya- manyan filaye na noma, ta yadda wurare zasu koma kore gwanin ban sha'awa.
Haka nan mota sakamakon haduwar kanana da manyan sassa ta zama mota ta yadda za a iya shiga a je wuraren da ake bukata, haka itaciya daga sassa manya da kanana, kamar rassa da ganye idan ba su samu tushe daga sauya guda daya ba, to ba za a iya taba samun itaciya guda daya ba, ta yadda za a iya amfana da ita ta hanyoyi daban- daban. Haka nan makaranta, ba tare da haduwar shugaban makaranta da malamai da 'yan makaranta ba, makaranta ba zata taba samuwa ba, haka nan ajin karatu ba tare da jaka da littafi da alkalami ba, ajin karatu ba zai samu kammala ba.
Haka nan fahimtar karatu yana bukatar natsuwa a kan abin da ake koyar da mutum, ba tare da wannan ba koyon karatu ba zai tabbatu ba. kamar dai na'urar daukar motoci dukkan karfinta ta mayar da shi ne a waje guda, ta haka ne take daukar abubuwan da take so ta kai wurin da take bukata ta ajiye su.
Tsakanin rundunonin sojoji guda biyu da suke fada, kawai rundunar da zata ci nasara ita ce, wacce ta kaucewa rabuwar kai da sabani a tsakanin juna kuma tana biyayya daga shugaba guda wanda ya san ya kamata, ta yadda zasu samu hadin kai mai karfin gaske a tsakaninsu, amma waccan rundunar da kowane daya daga cikin sojojinta yana wani abu daban da na dan'uwansa yake yi, tabbas ba tare da wani shakku ba, za a samu cin galaba a kansu.
Mutane 'yan kadan wadanda kansu yake a hade zasu ci nasara a kan mutane masu yawa amma kawunansu a rarrabe, labarin sojoji guda dari uku wadanda wasu 'yan fashi guda biyu kawai suka yi wa fashi kuma suka kwace musu makamai ya isa sheda a kan wannan al'amari na hadin kai da muke magana, a lokacin da aka kai wadannan barayi a kotu sai mai magana da yawun wadannan mutane 300, cewa ya yi sirrin nasarar wadannan barayi a kanmu shi ne sun kasance su biyu amma tare suke, amma mun kasance mu 300 amma ba tare muke ba. A yau manya-manyan matsaloli na duniya ana taruwa a wuri guda sakamakon tattaunawa a tsakanin masana a warware su, idan har hankali da shari'a suna karfafa wannan lamari na hadin kai da tattaunawa tsakanin juna, sakamakon haka ne cewa hankalin mutum guda ba zai iya warware matsala ba ta fuskoki daban-daban kamar yadda mutane da yawa zasu iya kallon matsala ta fuskoki daban-daban kuma su warware ta sakamakon musayar ra'ayi tsakanin juna.
Hakika hadin kai shi ne mabudin ci gaba da cin nasara a tsakani al'ummu Musamman ma musulmi.
TAMBAYA
Yakamata Musulmi Su hada kawunan su ??
YES or NO