No title

BAYANIN CIWON HANTA (HEPATITIS  YANDA AKE DAUKARTA DA SHAWARWARI GA WADANDA SUKE DAUKEDA CHUTAR.



                Chuta da magani

Daga shafin ma'asumiya Nigeria news updates

Tareda: Jibril Usman Sarki(08149953832)

Ya kamata a san cewa akan
samu kwayoyin ciwon hanta nau’in B
ko dai daga wurin mahaifiya yayin
da ake ciki ko yayin haihuwa, ko
kuma daga abokiyar zama wato
matarka, (wadda ita ma za ka iya sa
mata idan ba ta da shi), ko kuma
idan an taba maka karin jini a
asibiti, jinin da ba a tantance
lafiyarsa ba, ko kuma idan an taba
yi maka amfani da kayan kaifin da
aka riga aka yi wa wani mai cutar,
kamar kaciya ko shayi, ko allurar
kyamis da sirinji maras kyau da dai
ire-irensu.

To idan ka san wadannan, ya
kamata ka san cewa za ka iya sa wa
wasu, kamar matarka da ’ya’yanta,
don haka babbar hanyar kiyaye
shafa wa wasu ita ce ta neman ’yar
uwarka mai irin wannan matsala.
Ana haka ne a asibitin da aka yi ma
wancan gwajin, idan ka je ka yi
bayani, kamar yadda yanzu a
cibiyoyin karbar maganin sida akan
hada mai cutar HIb da wata mai
cutar a ba su shawara su auri
junansu don kada su shafa wa
al’umma.

Idan aka yi haka kuma idan ta samu
juna biyu sai a je asibitin a ji
ka’idojin kiyaye shi abin da ke ciki
daga kwayar cutar, musamman idan
an zo haihuwa da shayarwa, ciki har
da allurar riga-kafin kamuwa da
kwayoyin.

Sa’annan ya kamata ka san cewa, ba
kamar HIb ba, shi wannan ciwo,
yawanci, sai ka shafe rayuwarka bai
nuna wasu alamu ba, kwayoyin na
kwance, amma HIb kusan dole sai ta
nuna kafin a je da nisa. Don haka ba
wani magani taka maimaida za ka nema na
ciwon hanta na nau’in B a yanzu,
domin har yau babu maganin da dakasha zai kashe su.

 Idan ka fara jin wasu alamu na
rashin lafiya, kamar kumburin ciki,
zazzabi da canzawar kalar ido zuwa
ruwan dorawa, to a iya cewa ciwon
na hepatitis ya tashi, wato kwayoyin
sun farka kuma suna hayayyafa.

A wannan gabar Sai kayi kokarin ziyarta Asibiti da gaggawa domin ganin likita  dakuma kiyaye ka'idoji da shawarwarin da akabaka.

   Kowa dai yasan kwayar cutar Virus ita ke haddasa ciwon,sbd haka idan ya kamaka se taka tsan tsan da rokon Allah shi yaye maka ita.
Mdanmasaniskff@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post