ABUN TAKAICI MUSULMI NA TSAFI DON YA ZAMA WANI ABU!!

Kayi share domin wasu sugani su amfana
-----------------------------

---Inji Jagoran gaskiya [Sayyid Zakzaky]


""To wadannan fitine-fitine Malam, za ka sha mamaki a irin wannan zama
da aka samu ’yan musulmi, to bari ma in ce masu ma musulmin, in an je
lahira a san a ’yan wanne za su tashi. Wadanda imaninsu da Allah ya yi
rauni ya zamana cewa sun fi yarda da tsafi. Ba bambanci tsakanin kafiri
da musulmi a yin tsafi yanzu. Musulmi na tsafi don ya zama wani abu,
kafiri ma na tsafi, duk matsafarsu kuma daya. To tambaya ita ce, yanzu
har yaushe ne za mu zauna a cikin wannan hali? Shiru za mu yi mu ce
shi kenan Allah ya gyara?
Akwai wani muna magana da shi game da halin lalacewar da muke
ciki, sai yake cewa wai Allah zai gyara mana. Sai na ce, to kai kana ta
cewa Allah zai gyara, Allah zai gyara, akan zauna ne kawai Allah ya
gyara? Karanta tarihi ka gani. A wace qasa ce mutane suna lalace, suna
zaune abin su lalatattunsu, sai suka wayi gari duk Mala’iku sun sauko
sun sa fukafukinsu duk sun gyaggyara komai? In ‘Permanent secretary’
ya je ofis, kawai sai ya ga Mala’ika da fuffuke ya ce ‘you are not
permanent secretary again, I am Permanent now.’
Duk ’yan sanda masu cin hanci, duk su zo su ga cewa duk ‘yan
sandan, kowa ma yanzu da fuffuke. Sai duk kawai Mala’iku su gyara
gari. Haka ya taba aukuwa a tarihi? Bai taba aukuwa ba. Mune zai auku
a kanmu?

 Mu mu gyaru, to kana tsammanin za mu wayi gari ne kamar da safe
mutum ya bude qofa kawai, a ce masa kai ba ka sani bane? Kana barci
ai an zama ‘Islamic Republic’. Kawai sai ya duba ya ga komai, kowa ma
adili ne. Ina tsohon macucin nan? Sai a ce ai yanzu ya zama waliyyi!
Duk kawai an gyaru, duk kawai gyarau, kawai kowa ya gyaru kawai. Ka
duba sai ka ga kai ashe kai ma yanzu mutumin kirki ne! Ya taba aukuwa
ne a tarihi? Bai taba aukuwa ba!
Ko kuma wadannan ja’irai din, ranar maulidin da ta wuce, ranar
Alhamis na zuzzuba masu. In ma an ce na yi zagi, na yi din. Domin daga
cikin nau’in wa’azi in ya yi zafi yakan zama zagi. Kamar yadda Annabi
Ibraheem ya ce “Uffin lakum wa lima ta’abuduna min dunillahi.”
Na ce wadannan tsinannu, tsinannu, tsinannu, la’anannu,
la’anannu, fasiqai, fajirai wadanda suke mulkin qasar nan, Allah ya isa.
Allah ya isa, ba mu yafe masu ba! Allah ya fidda mana haqqinmu a
kansu.
Kuna tsammanin sune za su gyaru su zama mutanen kirki? Ka taba
karantawa a tarihi aka ce maka wata al’umma an sami wani azzalumi
yana ta cutar mutane, duk mutane suna shan wahala, talakawa na ta
wayyo Allah. Kawai ran nan a duba haka sai wannan azzalumin ashe ma
ya zama waliyyi, ya gyaru, sai kawai ya gyara komai. Ka tava ji a tarihi?
In da shi a gaya mana!
Ko tatsuniya ce aka ce ga ta gata nan ku. Aka ce ta zo mu ji ta. Aka
ce wata rana ne dai aka yi wani Sarki Azzalumi, yana ta tursasa talakawa
suna ta wayyo Allah, suna ta kuka suna Allah ka ba mu mafita. Yana
yanka mutane, yana shan jinni, yana tsafi, yana yanka jarirai, har ma da
a ciki ma yana cirewa. Kawai da mutane suka yi ta magiya, Allah ka
canza mana, haka kawai sai ya zama waliyyi. Sai azzalumin, waliyyau
kawai sai ga shi ya zama waliyyi, sai ya gyara komai sai aka huta, aka ce
masha Allahu, tsinannen jiya, gyararren yau. Ka taba ji?

Ko Tatsunniya ce aka ce an yi wani azzalumin Sarki, ya dinga tursasa
mutane, sai (kuma a dare daya) ya gyaru duk komai ya yi kyau. Sai aka
ce qurungus. To za a ce kai wannan tatsuniyar ba ta tatsuniyantu ba!


👇🏽-------------------------👇🏽

Ma'asumiya Nigeria News Update,  [Filin Jagoran gaskiya]


Wakilinmu Mahadi Tukur Almizan

         

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post