WATA SABUWA!! ASSIRI YA TONU AYAU:

 An Bankado Wata Sabuwar Dasisa Na Yunkurin Dakile Yiwuwar Bada Belin Shaikh Ibraheem Zakzaky Daga Fadar Shugaban Kasa....

Tare da Shafin Ma'asumiya Nigeria News Update 

Fassarar Abdullahi Isah Wasagu
Daga Shafin Da'irar Kaduna.

Ayyau nannen shafin kwamiti mai fafutukar tsara muzaharori da gangamin kiran a saki Shaikh Zakzaky da aka fi sani da "Free Zakzaky Committee" ta bankado wata sabuwar dasisar mahukuntan wannan kasa na zagon kasan dakile yiyuwar bada belin Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky(H).

Shafin mai suna "Reflection-online.com" ya rahoto cewa, a yanzu haka dai gwamnatin wannan kasa na bin dukkannin hanyoyi da za su iya bi, wajen ganin cewa Alkali mai sauraran karar da gwamnatin Kaduna ta shigar bai yi shari'a akan neman beli da Lauyan Sheikh Zakzaky Femi Falana ya shigar ba a gaban Kotun.

Idan ba a manta ba, a lokacin zamamen Kotun na baya, zama na kusa da karshe, mahukuntan sun bada wasu guragun hujjoji na rashin gabatar da Shari'ar, inda suka ce hakan ya biyo bayan wata 'yar hatsari da Alkali mai shari'ar ya samu.

A zama na karshe, harwayau Kotun ba ta zauna ba, inda mahukuntan suka kara kawo raunanniyar hujja na rashin wadatattun jami'an tsaron da za su bawa Shaikh Zakzaky kariya da kuma tawagar shugaban kasa da zai kawo ziyara Kaduna a wannan rana.

A cewar editan shafin, "Majiyar ta ci gaba da tabbatar mana cewa, suna ta kokari su yi amfani da dukkan karfin da suke da shi wajen ganin Kotun ba ta zauna ba a ranar da Kotun za ta ci gaba da sauraron karar a cikin watan Oktobar nan mai zuwa(7 ga watan Oktoba, 2018)."

Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa, "A hasashen fadar Shugaban Kasa, bata aminta da yanayin da sakamakon karar zai haifar ba, wanda take ganin cewa shari'ar ba za tayi daidai da muradun fadar ba, ganin yadda a sakamakon shari'o'in baya a birnin Abuja da kuma Kaduna, duka sakamakon sun goyi bayan Shaikh Ibraheem Zakzaky ne kawai da almajiransa ganin yadda Kotunan ke wanke su suna fita".

A wani yanki na tattaunawar sirri da shafin ta kawo daga fadar shugaban kasan, "Za mu zura ido ne mune kallon Kotuna suna wanke wannan mutumin da kuma sakinsa! Lallai da mun tashi aiki !". Wani yanki na yadda fadar shugaban Kasa ke tattuna yadda za dakile yiyuwar bada belin Shaikh Zakzaky.

Harwayau, majiyar ta shafin ta jiyo cewa fadar shugaban kasan ta fara tunanin cewa, gwamnatin El-Rufa'i ta Kaduna da aka barmata kes din bayan wanke Shaikh Ibraheem Zakzaky da Kotun Abuja tayi hade da bada umarnin sakinsa, to gwamnati ta gaza! Da yiyuwar gwamna El-Rufa'i ba zai iya aikin ba. Tunda ya yiwa fadar alkawarin amfani da 'yan Tauri, zauna gari banza da 'yan Kato-da-gora wajen kawar da Harkar Musulunci a fadin garin Kaduna, amma ya gaza.

A wani bange na majiyar sirrin da shafin ta jiyo daga fadar shugaban kasan, da kuma gwamnatin Jahar Kaduna, suna so suyi amfani da lokutan Tattakin yaumul Arba'een wanda ake gabatarwa a halin yanzu, wajen kawo rudani a tsakanin mambobin Harkar Musuluncin da kuma garin Kaduna, wanda wannan zai ba su damar gayawa Duniya dalilansu na kin kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky Kotu domin ci gaba da shari'ar.

A yanzu haka dai sun fara bawa jami'an tsaron da ke sintiri a cikin birnin Kaduna damar yadda za su haifar da wani yanayi wanda zai sa Kaduna ta rikice, ta yadda ba za a samu sukunin kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky Kotu ba a ranar 7 ga watan Oktobar nan mai zuwa domin ci gaba da shari'ar.

Idan haka bata cinma ruwa ba a wadanan nan hanyoyi da aka lissafo a sama, wata hanya kuma da suke tunani, ita ce su tunzura kungiyar Kwadago zuwa yajin aikin gama gari, wanda wannan ya biyo bayan kai ruwa rana da ake tayi na mafi karanci albashi, wanda akwai yiyiwar Kungiyar ta kira yajin aiki a ranar 6 ga watan Oktoba 2018, kwana daya ke nan kafi ranar da ake tunanin kawo Shaikh Zakzaky Kotu.

Idan ba a manta ba tun a ranar 2 ga watan Disambar 2016 ne, wata babbar Kotu a Abuja ta wanke Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa ta kuma bada umarnin a sake sa cikin kwanaki 45, amma mahukuntar wannam kasa har yau din nan suna ci gaba da kunnan uwar shegu da wannan umarnin, baya ga dasisosi daban-daban a lokuta daban-daban na ganin sun ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky ko kuma sun salwantar da rayuwarsa ta hanyar tsarewa.

Al'amari da Duniya ake ci gaba da yin Allah wadai da wannan bakin zalunci da ba a taba irinsa ba a Duniya. A cikin satin ma, a kasar Iraqi miliyoyin al'ummah na ta kafa hotunan Shaikh Ibraheem Zakzaky da Malama Zeenah da kuma wasu ba'adin kazantattun hotunan kisan kiyashin Zariya a zanguna daban-daban na hanyoyin masu tafiya filin Karbala suna ci gaba da Allah wadai da hukumomin Najeriya kan  wannan bakin zalunci da take ci gaba da yi.

Muna rokon Allah ya kara kare mana Malalm daga dukkan sharrinsu ya kara masa lafiya, ya kubutar dashi daga hannun wadan nan azzalumai.

Copy daga shafin da'irar kaduna

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post