ILIMI NE MAFI MUHINMANCIN ZIKIRI

Kayi share domin wasu sure amfana...


Inji Jagoran gaskiya {sayyid zakzaky}
Daga Shafin Ma'asumiya Nigeria News update a filinmu na (JAGORAN GASKIYA)  tare da Wakilinmu Mahadi Tukur Almizan.


Kuma ilimi (kamar yadda ya gabata akwai maudu'i ma a kan ilimi), to
shi ne muhimmi daga cikin wadannan Azkar din, wato shi ma nau'i ne
na zikiri, ko ma shi ne ma ya fi muhimmanci. Har ma a cikin magabata
akwai wanda ya daki qirji ya ce ma idan ana sa ran dare ya kasance
Lailatul Qadri, to mafi kyawun ayyukan wannan dare shi ne a raya shi
da muzakarar ilimi. Wato tunda yana ganin muzakarar ilimi shi ibada ne.
Saboda haka muzakarar ilimi a wannan daren shi ya fi ka yi sallah ma.
Za mu iya cewa kowane abu yana da muhallinsa ne, daya ba ya tsayawa
a muhallin daya. Ilimi da zikiri sun bambanta. In ka yi ilimi kawai ba ka
yi zikiri ba, to ba ka ma yi ilimin ba. In kuma ka yi zikiri ba ka yi ilimi
ba, shi ma ba ka yi zikiri ba, saboda duka guda biyun ne ake gwamawa,
ilimi da zikiri. Wadannan sune ABINCIN RUHI. Don haka ko da
kullum za mu hadu ne mu dinga maimaita abu guda, mu yi ta fada, mu
yi ta fada, to duk da haka nan muna ciyar da ruhinmu da abinci ne, muna
raya shi ne
[FILIN JAGORAN GASKIYA

Ma'asumiya Nigeria News update ]

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post