Kada kasake ka taimakawa Azzalumai Wajen Ruguza wannan kira da Sayytid Zakzaky (h) ya shafe Shekaru sama da 40 yanayi

Yi share domin wasu sugani su Amfana..

Sayeed Ibraheem Zakzaky (h) 


Ma'asumiya Nigeria News update Tare da wakilinmu: Jibril Usman Sarki


Da sunan ubangijin da ya karbi  rayukan Sayyid Ahmad da yan uwnsa a matsayin shahidai.
Sayyid ya kwashe Sama da shekara 40 yana kira azo abi tafarki ma daidaichi da kaucewa duk wani tsari da yasabama kur'ani sanan ayi bara'a ga dagutai (zazzalumai) Sayyid bai gusheba yana wayarda kan al'umma akan manufar wanan tafiya wadda bata nuna wariya ko fifiko a cikinta, sannan bata ware wasu ba'adin mutane ba, ba Dan izala ko darika shi yana kiran dukkan al'umma ne wajan ganin ansamu mafita duniya da lahira ga al'umma baki daya.

Sayyid shine yafara haska mana hanyar Ahlulbait (as) kuma yanuna mana matsayinsu dayin koyi dasu adukkanin al'amari, Sayyid baigusheba yana bamu tarbiya kamar yanyan cikinsa, har yanzu  duniya tasan matsayin Ahlulbait (as).

Ganin kiran Sayyid barazanane ga masu mulki akan zalunci da masu goyon bayansu, suka shirya kawarda Sayyid ta kowace hanya Amman Allah bai basu nasara ba, Amman a hakan basu dainaba suncigaba da bin almajiransa da dauri da kisa batareda wani dalili ba kai hattashi kanshi basu barshi ba, sanin kowa ne ankama Sayyid lokuta da yawa ana tsarewa Amman a hakan baigusheba yana kiran al'umma zuwaga tafarkin Allah.

Ziyarci shafinmu a facebook
www.facebook.com

A bangare guda kuma malaman duniya wadanda suka saida lahiyarsu akan duniya basu kyaleshi ba suna cigaba da tuhumarsa dayimasa kazafi da karya akan abinda suma kansu sunsan bagaskiyaba ne, kuma sun San kiranshi sarai kan gaskiya ne, Amman sabida zuciyarsu ta kekashe suntsayu kan ganin cewa wanan da'awa tashi batayi tasiriba kuma sai sun ruguzata.

Ya kai Dan uwa ka kasance cikin masu taimakawa Sayyid wajan cigaban wanan harka daidai karfinka dakuma iyawarka, kada ka kasance cikin wadanda suke kokarin ganin bayan wannan kira na jagora.

Kasani yanzu ba lokacin ganin laifukan junanmu bane ba kuma lokacin wasa sharholiya bane, muhadu muyi aiki tukuru wajan ganin jagoranmu yasamu yanchi shine babban aiki dayake gabanmu yanzu, da kuma cigaba da nunawa duniya irin zalunchinda akayimasa da almajiransa.

Mu kauda kai ga duk wani Abu da zaijawoma wanan harka rarrabuwa da rigima acikinta, ko wanenmu yana neman stira ne gobe kiyama to kada musake mu ruguza aikinmu garin hango laifukan wasu.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=335778547155371&id=160808741319020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post