_Dr. Sanusi Abdulkadeer kano
DAga:M.N.N UPDATES
Tareda: Jibril Usman Sarki
Tabbas hakane muna cikin barazanar Sojoji za su iya bullo muna ta ko'ina a gabanmu ne ko ta bayanmu, to amma kada mu manta cewa Allama Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky (H) a yanzu haka yana hannun azzalumai a kowane lokaci suna iya aiwatar da mummunan kudirinsu a kanshi, don haka ba zamu saurara ba, ba za mu raga ba, ba za mu fasa addininmu ba saboda wadannan azzalumai, wannan ita ce fahimtar da muka fahimta daga koyarwar gidan Manzon Allah (s.a.w.w), don haka idan wani yace da mu za a iya kashe mu, sai mu ce masa dama an gayawa Imam Ali Zainil abideen wannan, amma me yace ? "Atuhaddiduna bil maut ? Ma'ana; yanzu da mutuwa zaku tsorata mu ? Innal maut lana adaa, mutuwa a gurinmu al'ada ce, wa karamatuna indallahi shahada, karamarmu darajarmu a gurin Allah (t) ita ce shahada.
Saboda haka ya 'yan uwa masu girma idan muka dauki wannan karatun, to ba kawai allama Sayyid Ibrahim Zakzaky zai fito bane, a a za mu yi maganin zaluncin da ake a wannan kasar, karshen zaluncin da ake a wannan kasar yazo karshe. Abin da muke fada kuma muke kara fadawa Janaral Buhari mai takama da Bindiga kuma mai takama da cewa sai ya kashe mutane ne sannan zasu bi shi, to mu ba irin wadanda ake tsoratawa da mutuwa bane, mu ba irin wadanda ake yiwa barazana da mutuwa bane, idan yana jin cewa shi Soja ne, to mu kuma mabiya Imam Hussain (a.s) ne, don haka ya sani ba shi da Bindigar da zata iya hana mu abin da muka fahimta kuma muka rika a matsayin addini.
Wani bangare kenan na jawabin da Dr Sanusi Abdulkadir Kano ya gabatar a jiya Lahadi 28/10/2018, a lokacin kammala zangon farko na tattakin Arba'in na Imam Husain (as) A Nigeria.