Hukuncin kisa ga duk wanda ake tuhumar yana Musulunci a boye

Kayi shere domin wasu su amfana....



-Inji Jagoran gaskiya [sayyid zakzaky (H) ]



O
tare da wakilin Ma'asumiya Nigeria News update acikin filin /JAGORAN GASKIYA\ wanda Mahadi Tukur Almizan ke jagoranta

""Bayan an jarrabta ku da tsoro, da ciwace-ciwace da talauci da sauransu,
da qasqanci a hannun maqiya, sai kuma a jarrabta ku kuma da wadata da
iko. Shi ma jarrabawa ne. Shi kuma ya fi wahalar ma ci. Fakam da yawa
sai mutum ya ci jarabawar talauci ya kasa cin na wadata, domin in ya
wadata, ya san cewa wadatar nan daga Allah ne, ya ba da haqqin Allah a
abin da Allah ya ba shi, ya bauta wa Allah a yayin da yake da wadata
kamar yadda yake yi lokacin da yake da talauci.

To kuma har wala yau iko shi ma jarrabawa ce. Na wani ana ce masa,
"da kai da wane," Khalifa, ana gwada wani Malami ne da wani Sarki.
Aka ce tsakanin Malam wane da Sarki wane wa ya fi haquri? Sai shi
Malamin ya ce, "ah, wannan ai kai ba ka iya kwatantawa ba. Yanzu ana
iya kwatanta haqurin mai iko da maras iko?" In iko na hannunka, in
mutum ya ba ka haushi, me za ka ce? Kana iya cewa a wuce da shi
kurkuku, ko? To idan ba ka da iko fa? In wani ya zo ya ba ka haushi, in
kai talaka ne, ya za ka yi da shi? Ba ka da iko. Ka ga dauriyar mai iko ya
fi wahala a kan dauriyar maras iko. Ka ga ashe idan aka ba ka mulki, shi
ma jarrabawa ce babba, za ka yi tawali'u? Ko kuwa za ka ga kai yanzu
komai kana iya yi? Har ka wuce gona da iri! Ka ga duk jarabawowi ne.

Shi wannan jarabawan nan in an sami nasara, shi ma ya fi wahalar ci.
Fakam da yawa sai ya zama sai an ci jarabawa kafin a samu nasara. Sai
kuma a fadi baya cin nasara.
Kamar yadda ya zo cewa Manzon Allah ya taba cewa: Ba talauci nake ji
maku tsoro ba, wadata. Wadata nake ji maku tsoro. Domin Bani lsra'ila
da aka wadata su, aka ba su mulki, sai suka yi rige-rige, 'munafasa' a kan
abin duniya, har suka saki hanya. To, ina ji maku tsoron kada duniya ta
bumbunto maku a ba ku iko da dukiya, ku ma ku yi gasa wajen diban
duniyar, ku kuma ku koma kamar yadda suka kasance.

Kun ga kuwa wannan ya riga ya auku, ya auku sosai a wannan
al'ummar. Wannan shi ya sa ma al'umma ta rasa izza dinta ta koma baya.
Lokacin da musulmi suka mallaki duniya, sun sha shagali, an sha
shagulgula! Aka yi ta abubuwa maka Malam!
Nakan ba da wani misali na wani abin da na karanta a wani littafi wanda
yake shi kuma ba musulmi ya rubuta ba. Yana fadin yadda musulmi
suka sha shagali a Andulusiya. Aka ce wani Sarki ya nishadantu, ya ce
ina tunanin a tara mawaqa su yi waqe na abinci. Su waqe abinci. Sai aka
ajiye kwanan wata aka ce kaza ga wata za a yi gasar waqe, duk mawaqa
su zo. Waqen abinci kawai za a yi. Mawaqa kuwa suka hadu, su wajen 40.

Aka ce mawaqi na daya ya zauna ya waqe wani iri na liyafa, na abin
da ba a taba gani ba. Ya ce duk irurrukan ma na zinari ne. Tsakiyar an sa
gasassahen nama, an kewaye shi da gasassun kaji, a gefe kuma qwayaye
ne. Nan kuma an zuba wani mai kamar azurfa yana narai-narai. Can
kuma ga... Ya dinga dai bayani dai! To ai Sarki sai ya kada kai, ya ce to,
gobe wannan abin da ka fadi shi za a ci. Aka kira Mawaqi na gaba shi
kuma ya zo ya yi duk abin da ya sawwala, Sarki ya ce kai kuma jibi abin
da ka fadan nan shi za a ci. Mawaqi na gaba ma ya jero nasa. Sai da aka
yi mawaqa arba'in. Duk abin da suka sawwala shi aka ci, kwana arba'in
ana cin shagali.
Wannan a Andulusiya aka yi wannan, lokacin da musulmi suka kafa
mulki a can. Suna wannan shan shagulgulan kafirai suka yi shiri suka fidda musulmi gaba daya daga Turai. Da a ce ba su yi wannan abubuwan
ba, da Turai din nan da suke ta balbalo mana bala'i, wannan Andulusiya
Din su suka fi ci gaba a qasar Turawa. Sune duk suka gano sauran
qasashe. Wannan shekarun da suka riqa zuwa bincike-bincike din nan,
to a nan ne suka gano tsibirin Amerika. Daga nan suka fara wayewa
suka yi qarfi. Daga baya ne Ingila da Faransa suka yi qarfi fiye da su,
bayan wadansu yaqe-yaqe da suka yi. Amma da su ke da qarfi, suka je
suka gano Amerika suka kai addinin Kirista, suka je suka samu mutanen
da duk abin da suka ce masu su yi, shi suke yi. Suka yi ta yi wa
matansu, suka karkashe su suka sabautar da su suka kwashe
dukiyoyinsu suka yi ta ta'asa.

Aka ce sun kama wani Sarki, wani Sarkin irin jajayen Indiyawa din nan.
Da suka riqe shi suna ta azabta shi. Sai ya nuna masu wani gida, ya ce in
na cika maku (gidan) nan da zinare za ku sake ni? Suka ce eh. Sai ya ce
a gaya ma jama'arsa, da mai abin wuya da mai abin kunne da mai komai.
Sai da ya cika wannan gidan da zinari. Aka cika wa Turawa shaqe da
shi. Don su sake shi. To kun san abin da suka yi wa wannan Sarki? Qona
shi suka yi da wuta! Bayan sun kwashe zinarin, suka qona shi qurmus.
Wannan ta'asar da Turawa suka je suka yi kenan. In da musulmi ne suka
je wannan wurin, me za su kai? Ku gaya mini? Da duk mutanen
Amerika musulmi ne. Saken da musulmi suka yi da suka kama wannan
ariya din shi ne sai suka shiga shan shagali, da shagali ya yi shagali,
wadannan kafiran suka zo suka kore su. Aka ma hana yin addinin
Musulunci a qasar Ispaniya din gaba daya. Aka yanke hukuncin kisa ga
duk wanda ake tuhumar yana yin Musulunci a boye.
In ana watan Ramadan aka ga alamar ba ka ci abinci ba, sai kawai a kai
ka a ce ana tsammanin wannan yana azumi ne, sai a ce a qona shi da
wuta, qurmus kuwa! Da haka suka hana addini, addinin da ya zauna nan
ya yi mulki, ya yi shekara wajen 600, aka fid da shi. Saboda shagali da
aka riqa sha daga baya. Kuma wadannan fitinoni ne duk daban-daban
ake jarraba mu su�"".
[TASIRIN DABI'U]
kucigaba da kasancewa tare da ma'asumiya Nigeria news update

tare da Mahadi Tukur Almizan 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post