Har Yanzu bakusan muba!!

Ma'asumiya Nigeria News Update


to bari kuji ko mu su waye..........

Mune musulmai mabiya koyarwar gidan Annabta.

Mune masu kira abi Allah da manzonSa (s) a kuma yi tawaye ma duk wani tsarin da yaci karo da nasu.

Mune masuyiwa addinin muslumci adalcin tsage gaskiya a cikin sa a duk inda muka ganta bangaren Shi'a ko sunnah.

Mune masu kira zuwa ga adalci da kuma yaki da zalumci.

Mune wadanda al'umma ke tsananin ki, muke kuma tsananin tausayi da kaunar su.

Mune wadanda ake zalumta tsawon tarihin musulumci ta hanyar zagi,tsana,duka,kora,dauri da kuma kisa,amma hanyanzu bamuyi ramuwa ba badan bama iyawa ba sai dan hakan ba tarbiyyar addinin muslumci bace.

Mune masu umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna.

Mune wadanda a kullum ake koya mana aiki da hankali kuma wautar wawaye bata mun canza ba.

Mune masu daukar duk wani wanda ya furta la'ilaha illahu dan uwa kuma masoyi,wanda bai furta ba kuma abun kyautata mawa domin ya fahimta.

Mune masoya duk wani mai gaskiya mumini kuma makiya duk wani munafiki azzalumi.
Mune masu gwagwarmayar kawar da tsarin shaidan da tabbatar da tsarin Allah ko da kafirai da munafukai da jahilai basaso.

Mune masu ashura da tattaki da kudus da mauludi.

Mune masu husainyya bakiyatullah Zaria da fodiya da darul rahma da film village.

Mune aka shewa 'yan uwa maza da mata da kananan yara,wasunsu aka konasu da ransu,wasun kuma aka zuba rami aka bizne alhali akwai wadanda basu karasa mutuwa.

Mune almajiran sayyid Ibrahim elzakzaky (h).
Wanda babu laifin fari bana baki akaje da motocin yaki aka kashe masa almajirai har da 'ya'yansa uku yace ayi hakuri.

Shine wanda ya shafe mafi yawan shekarunsa ya hidima ma addinin Allah ba dare ba rana.
Shine wanda ya dauki wahalhalu da matsi iri-iri kama daga zagi,takura,karya ,sharri,duka,Sara da takobi da adda,harbi da kibiya da harsashi, kamu dauri,rusa gida da konawa kashe mai 'ya'ya da dai cin zarafi kala amma duk yayi hakuri yace muma muyi hakuri.
Ka kiyasta daga nan kagani shin hakan yayi daidai da abunda ake fada maka akan mu?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post