Yan Shi'a Sun Fara tattaki Zuwa Zaria ko Abuja a jiya


Kayi shere domin wasu sugani su Amfana 

Tare da wakilinmu mahadi Tukur Almizan


 Daga Ma'asumiya Nigeria News update


A   Alhamis 25 October yan Uwa Musulmi mabiya mazhabar Shi'a a Nigeria, Almajiran Mlm Sheikh Ibrahim Zakzaky (h) na Yankin kano da kewaye suka fara Tattakin Arba'in din Imam husain (a.s) kamar yadda Suka sabayi kusan shekara 20 da suka wuce. Tattakin na Kano Wanda Wakilin mabiya mazhabar Shi'ar na Kano sheikh Sunusi Abdulqadeer ya jagoranta,

Dubbunan tururuwar Mutanene masu yawan gaske  Suke wannan tattaki suna dauke da tutoci masu dauke da kalmar LABBAIKA YA HUSSAIN suna rera wakokin juyayain ashura da kuma kiran gwamnati da ta gaggauta sakin sayyid zakzaky . Anfara wannan tattaki  wajen misalin karfe tara 9:00am, tattakin ya gudana kuma yana kan gudana cikin tsari da nizami Kamar yadda malamin nasu ya tarbiyantar dasu,

 Bayan doguwar tafiya da Suka shafe awoyi sunayi sun wuce gadar na'ibawa [fly over],
Idan Mai karatu bai mantaba, a dai-dai wannan gadane gwamnatin jahar kano ta tura jami'an tsaronta suka sheqar da jinin Mabiya mazhabar a bara wajen gudanar da irin wannan ibadar da sukeyi, aka kashe muminai a lokacin nema aka shahadantar da shahidah husaina Nalado, yarinya yar makaranta data....

 Bayan anwuce wannan gada
Sannan aka yada zango domin yin salloli da cin abinci, inda malam Abdulhamid bello wakilin mabiyan mazhabar A zariya  ya jagoranci yan uwa akai sallah, cikin ikon Allah har sanda aka yada zango nafarko wannan tafiya bata gamu da wani cikas ba daga jami'an tsoron Nigeria kamar yadda sukayi a shekarar data gabata.

Tattakin sunayin shine kamar yadda wani mabiyin mazhabar ke gayima wakilimu cewa: domin nuna Alhininsu da damuwar su bisa GA zaluncin da akayiwa iyalan manzon Allah (saww)  filin karbala,  daga bisani akajasu akasa acikin zafin rana babu takalma suna tafiya.

ANKAMMALA LAFIYA
Ya zuwa yanzu ankawo zangon karshe, sai kuma Allah yakaimu gobe za'acigaba Insha Allah.

Kuci gaba da kasancewa da shafin Ma'asumiya Nigeria News Update domin Samar muku nagartaccin rahotanni da labarai na ilimantarwa da fadakarwa

 *©Mahadi tukur almizan wakilin ma'asumiya Nigeria News update*


https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=335096167223609&id=160808741319020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post