Ⓜa'asumiya Nigeria 🇳🇬 News Update
Tareda Mahadi Tukur Almizan*
"Lallai ne babu wani yanayi dake tabbata walau medadi ko maras dadi,
Hakanan Zalunci ma bazai tabbata ba, kamar yadda Allahu Subhanahu wata'ala baya zalunci, domin shi Adalin Sarkine, haka kuma bai yadda da zalunci ba kuma baya goyon bayan Azzalumi,
Abin Mamaki Awannan lokaci da muke ciki, da zalunci yayi yawa matuka, Seka ga Mutanen da suke Ikirarin cewa su Musulmaine Amma sune gaba wajen goyon bayan Azzalumai, kawai saboda wa'inda Ake zalunta ba fahimtarsu daya ba, ko kuma Akwai wata kiyayya da ke Atsakaninsu wadda tasamo Asali da dadewa,
Shin dan uwa Musulmi, A ina ne Addinin Musulunci ya yadda ka goyi bayan Azzalumi, Mun san dai Musulunci daya ne, Babu inda Allah ya yadda da Agoyi bayan Azzalumi, Kuma dukkan Annabawan Allah babu wanda yayi da'awar hakan,
Zaka sha Mamaki idan kaga dabbobi Suna Kokarin Ceton Ran yan uwansu, koda kuwa ba jinsinsu daya ba, Amma hakan Nada Wuya acikin Al'ummar mu tayau, Duk da Fifikon da Allah yayi Atsakanin Dabbobi da Mutane, Shin Meya kawo hakan?
Dan uwa, karkasake duniya da Abinda ke cikinta Surudeka Kamanta da Makomarka ta Gobe Kiyama,
Idan har Aka Zalunci Wani, Wannan ko kowane irin Mutum Ne Kuma kowane irin Addini yakeyi, Domin Allah daya Halicceshi baya halicceshi bane domin Wata Halitta ta Zalunceshi, to wajibi ne Akanka ka barranta kanka daga Wannan Zalunci,
KASANI TunatarwaFA KO KASO KO KAR KASO ALLAH ZAI TEMAKI RAUNANA, KUMA ZAI KASKANTAR DA AZZALUMAI
#You_No_Need_To_Become_A_Muslim_Or_Christians_To_Stand_For_Justice.
*#Humanity_First*.
*@Mahadi Tukur Almizan.*
Tags:
Tunatarwa