Maganganu Cikin Hikimomi

Ku Ziyarci Shafin MA'ASUMIYA domin Samun Ilmantarwa da fadakarwa.
DUKIYA A MATSAYIN AMANAR ALLAH.

       Daga shafin ma'asumiya Nigerian News Updates

Tare da wakilinsu Idishia Jos

    "Dukiya da 'ya'ya su ne adon rayuwar duniya, kyawawan ayyuka na gari sune suka fi lada gun ubangijinka kuma su ne mafi cika. {kahfi: 46}" Amana ce Kan mutum ya zama zai iya canza bakin cikin sa da na mutane su koma farin ciki. Da wannan ne za'a bawa rayuwar burin ci gaba domin samun rayuwa mafificiya. Da wannan ne za'a iya dakatar da rikici da jayayya da fada da miyagun halaye, a canza su da so da abota da kauna, kuma a hana mafi yawan gidaje rushewar auren su, kuma a kosar da mayunwata, a warkar da marasa lafiya, a warware matsalan masu matsala, a tseratar da masu neman mafaka, a kawar da talauci da fatara.

Kai da yawan mutane ma za'a iya tseratar dasu daga mutuwa a canja musu matsalar su da tsoron su da zaman lafiya da aminci da samun saukin rayuwa da sararawa a cikin Al'umma. Da wannan ne za'a iya sanya ci gaba da kawo habaka a cikin lamarin kasa da Samar da rayuwa mai kyau da nishadi. Amanar Allah ce zata iya kawo daukaka a duniya da lahira kuma da taimakon wannan rabautar ne za a iya sayan lahira da kare mutuncin kai dana wasu ma kuma a samu amfani da za"a iya kaiwa ga ni'imar lahira mai yawan gaske.

Hatta ma da wannan kokarin ne za'a iya samu matsayin "Kokari a tafarkin Allah" ga kai da Addini da kuma wasu ma. Da taimakon wannan daukakar ne da girman darajar duniya da lahira ne za'a iya samun yardar Allah da yardar Manzon Allah. Kuma ka samu haduwa da manyan waliyan Allah da ziyarar dakin Allah da kaburburan Ahlulbaiti (as), da kuma Isar da sakon kur'ani da Ahlulbaiti zuwa ga duk fadin duniyar nan.

Dukiya a matsayin amanar Allah a hannun mu to zamu iya sanya ta zama wata hanyar samun yardar Allah madaukaki, kuma zamu iya kusan ci da Allah mu zama masoyan sa na hakika. amma Idan muna kallon dukiya a matsayin hadafin karshe da muke buri muke kauna, to a wanna lokacin ne dukiya zata zama kamar dan marakin lokacin Annabi Rahma da zai kawar da mutane daga shiriya, da shiga yin alfahari da fajirci da takama da jin kai.

A nan ne sai a samu rabuwa da kiyayya tsakanin masoya da abokanai da makusanta da sauran mutane, rayuwa ta zama battada ma'ana da manufa, wahala ta mamaye sauki. Dukiya abune ta jarraba mutum domin sanin Yaya kuma daga ina aka samo ta, kuma yaya ko ina za a sarrafata. Dukiya abune na amfani matukar gaske da saukin samun lada wacce za a iya amfani da ita don gina Addini da duniya, in kuwa ba haka ba to zata zama wahala da bala'i ga mai ita da musiba ga wa su.

Imam Ja'afar Sadeeq (a.s) yace: Dukiya ta Allah ce madaukaki da ya sanya ta ajiya a gun halittunsa kuma ya umarce su da su ci ta da tsakaitawa, su isha da tsakaitawa, su daura da tsakaitawa, su yi aure da ita da tsakaitawa, su hau ta da tsakaitawa, su mayar da abinda ya rage ga talakawan muminai, duk wanda ya ketare hakan to duk abin da yaci haram ne, abin da ya sha daga gare ta haram ne, abinda ya daura daga gare ta haram ne, abinda ya aura da ita haram ne, abin da ya hau da ita haram ne.
{biharul anwar: j ¹03,sh¹6,h74}.
***
     #FreeZakzaky

     #Freedom4Zakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post