_cewar Muhammad Al'hassan Kano
A hirar su da Wakilin Ma'asumiya Nigeria News Updates
Zaidu Suleman Shi'a.
Mai karatu zai so Sanin sunan ka,
Na'am da farko sunana: Muhammad alhassan ni mazaunin garin {Kano} ne a unguwar {Rijiyar Lemo,
*Yadda Nafahimci Harkar Islamiyya*
To Alhamdulillah da farko nidai ba a wannan harka aka haifeni ba, kuma bana ra'ayinta kwata kwata""" Bilhasalima ina ɗaya daga cikin mutanen da suke adawa da wannan kira sakamakon irin yanda ake. Yaɗa maganganu da yawa akan wannan kira,
Wasu lokuta Ma harda mu ake yaɗa irin wannan maganganu dana gaya maka,Bana mantawa wata rana yan'uwa sun taɓa shirya wani frograme na maulidin sayyda zahara (a.s)
Anan unguwar ta Rijiyar lemo, naje gurin lalle a ranar akwai wanda saida muka daɗe muna muhawara dashi akan ita kanta shi'ar amma cikin ikon allah Dukda inajina da ɗan' ilimi na alokacin saida ya kayar dani, wato ya fini hujjah tun daga ranar nasan cewa lalle jahilci bashine ya kafa waɗan nan mutane ba,
Haka dai na fara bincike akan wasu abubuwa waɗanda alokacin da muke tattaunawa da wannan ɗan'uwan danakegaya maka mun taɓo janibobi masu yawan gaske da ban mamaki da tausayi,Akan abubuwan da akaiwa Ahlil"baiti (a.s)
Na cigaba da bincike da kara saka ido akan duk wani motsi na yan'uwa kama daga maulud suke ko wani muzahara da kuma cigaba da bincike na ilimi wato karatu haka dai mukai ta tafiya inakara fahimtar abubuwa
Sosai ina rabe karya da gaskiya saɓanin ada sanda muna malikiyya ana sanar damu cewa duk abinda ya faru ya riga ya wuce kada muyi bincike hakadai zuciyata taita saƙa mini cewa anya kuwa akwai kanshin gaskiya anan???
Saboda ita gaskiya ba'a rufeta buɗeta akeyi mai neman ta ya ganta kuma ƴa bita amma anan anhanamu buɗeta ma balle muganta balle mu bita,!!! Lalle hakan ya ƙara mini kwarin guywa akan cigaba da neman shiriya ta gaskiya bata kwane kwane ba,
saboda duk abinda za'a ce abari to lalle zai wahala idan babu alamar tambaya???Haka dai naita ta tafiya na raba zuciyata gida biyu yan' shi'a nada gaskiya can kuma saita ce dani kai hanya kuwa???
Ana haka kwatsam saina ci karo da wani karatu na wani babban Malami Akano :Sheikh musal kasuwini sheikh malam nasir kabara>>>>>>
Wanda yaƴi akan wata musiba data faru Lokacin Annabi {S} yana halin Rashin lafiya wanda malamai na hadisi suke kiran ranar masifar ranar al"khamis ta ranar 24/ga watan safar. Wanda malamin yayi bayani akan Cewa Annabi (s) yace sahabbai su kawo masa tawada da alƙalami da abin da za'ayi Rubutu Annabi {S} ya rubutawa al"ummah abinda idan tarike to bazata taɓa ɓacewa ba,
Amma wasu ba'adin sahabbai suka hana hakan yasa naji araina cewa lalle shi'a suna kan gaskiya,Sosai da sosai tun daga wannan lokacin na ƙara gasgatawa cewa shi'anci shine shiriya saboda Nayi nazari sosai sahabban da suka hana Annabi (s) wannan abin rubutun sune ake yiwa shi'awa sharri da suna zaginsu.!
Harwala yau sune ake karewa ake tozarta wasu sahabban da suka dake gurin cika umarnin Annabi (s)Tun daga wannan karatu dana saurara na ƙara yaƙini akan wannan harka, na kuma sallama ɗari bisa ɗari na daina wani kokonto, akai!!!
Wakilinmu>>>::
Akaramakallahu ko zaka yiwa masu karatu bayani akan wane irin jarrabawa ka gamu da ita alokacin da ka fahimci shi wannan kira da kuma kalubale daka fuskanta tun daga lokacin har'zuwa yanzu. ???
Na'am.
e to na fuskanci jarrabawa kalakala dayawan gaske " amma zanyi maka ne ataikaice, kamar abu uku zuwa hudu zanyi maka bayani
na farko shine {1}
Abokaina, cikin gidanmu, da kuma makaranta, da gurin kasuwanci!'.
Abokaina da daman gaske sun gujeni sosai! domin akwai wani lokaci bana mantawa Ni'ina son zama dasu duk da nasan basa sona amma ya zama iɗan naje gurinsu to baza'ace na tashi ba, saidai kawai a ɗakko wani firan mai ɓata rai, don kawai a ɓata mini rai saina tashi nabar gurin tun bana ganewa har'na fara nage cewa zama ɗani ne ba'a so!Ta fuskacin abokai kenan,,,
sannan acikin gida ma na fuskanci makamancin irin wannan saboda agaskiya ina godiya ga allah azurtani da samun mahaifiya wadda bata son ɓacin raina kuma ta kasance tana yi mini addu'a duk da bason harkar take ba, amma bata takura mini akan saina daina harkar,Kawai ita addu'ar ta akaina kullin shine idan dai dai ne to allah ya tabbatar dani idan kuwa ba daidai bane ba, allah ya ganar dani haka nata shan jarrabawa acikin yan'uwana sukan nuna mini kyama sosai amma duk da haka ni kuma sai nake nuna musu banma san dani suke ba,
Akwai lokacin da mukai tattaki daga kano zuwa zariya a shekarar2015 wanda har' jahiiyya ta saka mana bom aka samu shahidai ansamu wasu dayawa daga cikin yan'uwana na jini wadanda suka zo suka samu mamanmu akan meyasa tabarni na fita???Ta basu amsa ne da subarni nayi abinda na fahimta suma suyi nasu,
Haka dai mukaita tafiya da da damuwa har' aka gudanar da waki'a ta zariya daga nanne na fara fuskantar kalubale a gurin aikina Amma cikin ikon Allah har'yanzu da muke wannan firar dakai malam zaidu wallahi ban fita ba, Ina barar addu'a daga yan'uwa akan haka,!
Wakilinmu>>>>
Akaramakallah ko kana da wani kira da kake dashi ga sauran al"ummah musamman ma yan'uwa mabiya mazhabar jafariyya ???
e tabbas inada kira ga yan'uwa cewa muji tsoron Allah musan menene ya hau kanmu kuma meya dace muyi??? Koba komai addini kira ne musan dame zamu kira mutane wadanda basu fahimci wannan kira ba, ina nufin Saboda tabbas tafiyar ahlil-bait (a.s) tafiya CE da dole saida ilimi ake iya yinta idan babu shi lalle bazata yiwuba, akan neman ilimi kenan,
Saboda jahilci ne ke damun mutane shine yasa suke kiyayya damu wasu kuma son xuciya ne Ammma gwargwadon yanda muka dauki abin gwargwadon yanda zamu samu magoya baya!!!don haka yan'uwa mu dage da neman ilimi
Wakilinmu>>>>
akaramakallahu wane kira kake dashi ga wannan hukuma ta Nigeria ??? ganin yanda aka aukawa jagoran yan'uwa musulmi wato yan' shi'a da kisa da kamu da rushe guraren ibada da kuma cigaba da tsare jagoran yan'uwa musulmi sheikh ibraheem zakzaky har' na tsawon shekara uku ba bisa ka'ida ba, wanda har' wata babbar kotu ta Nigeria ta bada umarnin a gaggauta sakin sa dashi da mai dakinsa amma har' yanzu ba'a cika umar nin kotun ba. wana kira kake dashi akan wannan lamarin???
Kirana guda daya tak kuma babu qari shine kawai su gaggauta sakin mana jagoranmu da gaggawa batare da wani sharadi ba,!!!
Alhamdulilah muna godiya sosai malam Muhammad alhassan
Allah ya saka da al'khairi malam
Daga wakilinmu na Kano Zaidu Sulaiman Shi'a
Ma'asumiya Nigerian News Updates
Tags:
Labari Na
