Rigimar Falasdinu ba ta addini ko jinsin ne ba- Sheikh Zakzaky



By Mas'udu Dan Masani Shinkafi Jul 30 2015


Rigimar Falasdinu ba ta addini ko jinsi ne ba - Sheikh Zakzaky...

Jagorar kungiyar ’yan uwa Musulmi mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ce rigimar da ke ci gaba da faruwa a tsakanin Falasdinawa da Yahudawa a kan mamayen da Isra’ila ke ci gaba da yi, ba ta takaita a tsakanin mabiya addinai kawai, ko kabilar Larabawa da ta Yahudawa ba, ya ce rigima ce a tsakanin gaskiya da karya da adalci da zalunci.

Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ya bayyana hakan a Abuja a yayin taron tunawa da mutum 34 da ake zargin sojoji da bude musu wuta a yayin muzaharar Ranar kudus a bara, ya ce mutum 14 daga cikin 34 da aka kashe, sun rasa ransu ne bayan an kai su bariki sakamakon azabtarwa da hana su abinci, ko harbinsu da bindiga, ciki har da ’ya’yansa uku Ahmad da Hameed da Mahmud kamar yadda wasu da suka tsira daga cikin wadanda aka kama suka tabbatar.
Uwargidar malamin kuma mahaifiyar ’ya’yan uku da aka kashe, Malama Zeenatu Ibrahim, ta ce abin da ya faru da ’ya’yanta da sauran mutum 31 da aka kashe, na faruwa ga al’ummar Falasdinu a kullum inda sojojin Isra’ila ke yi musu, sai dai ta ce bambancin shi ne, su mamatan 34 sojojin da ya kamata su kare su ne suka aikata hakan gare su ba na abokan gaba ba.


https://maasumiya.blogspot.com/2018/06/mai-gidan-gilas-bai-dace-yayi-wasan.html

  • Babban bako mai jawabi kuma Babban Limamin Babban Masallacin birnin Washington ta kasar Amurka, Sheikh Muhammad Al-Asi, ya ce kasar Isra’ila wadda Turawa suka kirkiro bayan Yakin Duniya na Biyu, na amfani da tasirin jarin da take da shi a cibiyoyin kudi na duniya da manyan kafofin watsa labarai, sai kuma daukar nauyin wasu ’yan majalisar dokoki a manyan kasashe, wajen cimma burorinta da suka hada da mamaye filin da ya dangana da Kogin Nilu a bangaren Larabawan Afirka kadai.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da shugaban Hukumar Kare Hakkin Jama’a ta Najeriya, Farfesa Chidi Odinkalu da Sheikh Muhammad Turi da Dokta Abdullahi danladi da Farfesa dahiru Yahaya da kuma Hajiya Bilkisu Yusuf da sauransu, yawancin wadanda suka gabatar da jawaban, sun bukaci a aiwatar da shari’ar adalci a kan kashe mutum 34 da har zuwa lokacin taron, babu sakamakon bincike da Gwamnatin Tarayya ta lokacin ta ce ta kaddamar.
A yayin zuwarsa wajen taron, ayarin Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi zargin musgunawa daga sojoji a hanya, kamar yadda wani na kusa da shi Dokta Abdullahi danladi ya bayyana wa manema labarai a wajen taron, inda ya ce a daidai lokacin da malamin ya bar garin Jere a kan hanyarsa ta zuwa Abuja, wasu sojoji sun sha kan ayarinsa a cikin motarsu, inda suka daga musu hankali tare da bukatar su fito daga cikin mota bayan sun tsayar da su, ba tare da yi masu tambaya ko sanin ko su wane ne ba. Sai dai a martanin kakakin sojin Najeriya Kanar Sani Kukasheka ya musanta zargin inda ya ce malamin ne da ayarinsa suka tsayawa a wurin binciken motoci na sojojin su kuma suka bi su a baya. Y ace duk da kalaman tunzurawar da almajiran Zakzaky suka yi musu sojojin sun nuna dattaku wajen kin tanka musu, kuma hakan ne ya sa ba a samu tashin hankali a tsakaninsu ba.

Ma'asumiya Nigeria news updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post