KUYI GAGGAWAR KIYAYE FACEBOOK ACCOUNT DINKU DAGA HACKERS


Daga (M n n u)

By Mas'udu Dan Masani Shinkafi

Assalamu alaikum, biyo bayan yawaitar kutse (Hacking) wa accounts din Yan-uwa a facebook, Misali Account din dan uwa SA'ID HARUNA) hakan yasa nayi yunqurin tallafowa da abinda na sani game da wannan harka, da fatan Allah yasa ya zamo mai Amfani:

Duk wani Hacking da za'ai a Duniya, ya ta'allaqa ne ga Abubuwa 2: IP address (Internet Protocol) da kuma PASSWORD!
Domin yin Hacking Facebook din mutum, kanada buqatar USERNAME da PASSWORD dinsa, amma samun Username baida wahala, sabida mafi yawa zakasameshi a Timeline din mutum, matsalar itace Password!

YANDA ZAKA KIYAYE ACCOUNT DINKA:
1: Ka hada Password mai wahala: ya zamana Password dinka yakai haruffa 8 ko sama da haka, ya zamana ka chakuda haruffa da lambobi, kada ka saka sunanka, sunan dan-uwanka ko wani makusancinka, kuma ka chakuda Upper-case da Lower-case (Manyan baqi da qanana) misali: HV3P7br0, ka sani, iya tsawon password dinka, iya wahalar da zai ba Hackers wajen maka kutse.

2: Akwai wani tsari na REMEMBER-PASSWORD dake kan Opera mini da browsers din, a bisa wannan tsari, duk sanda kai logging a wani shafin internet ka sanya User name dinka da password, zasu ce maka: Remember Username and Password? Idan ka danna OK, shikenan zasuyi saving dinsa, duk sanda kahau facebook, zai dinga budewa Automatically ba tare da buqatar ka saka Pasword ba!
Haqiqa wannan tsari nada Hatsari, domin duk sanda wani ya dauki wayarka, da zarar ya bude opera, zai iya hawa account dinka, hakanan in ka siyar da wayarka, ta fadi/aka dauketa! Don haka kada ka dinga zaban wannan tsari, idan kuma ka zabeshi, to ka gogeshi ta hanyar: OPERA=>SETTINGS=>PRIVACY=>REMEMBER PASSWORD=OFF/NO/UNSELECT! Sannan sai ka dawo qasa zakaga CLEAR PASSWORD=>YES!

3: Akwai Hackers dake turo da message na shirme (Spam/Trujars/Trash), duk sanda kaga message daga mutuminda baka sanshi ba, ko kaga Alamun ba dan Qasarka bane, to kada ka bude, in ka bude kuma, kada ka masa Reply, da zaarar ka masa Reply, zai iya samun Daamar kutse wa account dinka!
Yanzu abin ya shigo Nigeria sosai, so ku kula da irin matayen nan dake turo messages: Hello/Hi, zaku gansu da turanci suke, sannan profile dinsu is un complete!
4: Akwai Applications da daama da zaka shiga, ace maka ENTER-YOUR FACEBOOK USER NAME AND PASSWOR: # Kada_ka_sake_ka_rubuta ! Sannan akwai sites da zakaga musamman in kahau Facebook, zasu ce meka:

WE WILL USE YOUR FACEBOOK SERNAME AND PASSWORD! To kada ka sake ka amince, ka fice kawai, da daama, sune suke sanya hotunan Baatsa, rubuce rubucen banza a profile din mutane, domin duk sanda ka amince musu, shikenan sunada daamar Posting a profile dinka, Tagging Friends dinka da tura musu Messages!

5: Ka dinga sake Password dinka duk wata, kuma ka dinga hada password da zasui wahalar chinka!

6: Duk sanda zaka sauka a Facebook, ka dinga LOG-OUT kafin ka rufe browser dinka!

7: Kada ka dinga Log-in (hawa Facebook) ta computer kampani, Cafee, public, wayar wani e.t.c, idan kuma ka hau, ka tabbata kayi log-out kan ka sauka, in so samu ne, da zaarar ka dawo gida, to ka sake password dinka!

8: kada ka dinga Accepting Friends da baka sani ba, Musamman kaga India, China ko wata qasar waje dai, ko kuma kaga profile dinsu bai cika ba, kaman kaga suna ne kawai, amma ba Details din mutum! Ka kiyayi irin wadannan Profiles din, dayawansu Hackers ne!

A duk sanda kayi sakaci da Account dinka, har wani yayi yunqurin hada Password dinka, da zaarar yayita trying, Facebook zasui blocking Account din for security, sannan zasu sanar dakai duk sanda kazo Hawa FB, zasu buqaci ka sake Password!
Anan zanso inba Yan-uwa shawarar: Idan ka bude FB dinka ne da Email, to ka tabbata email din na aiki, kuma ka kula dashi sosai, domin duk wani aiki da ya shafi Account din, will be run on you email.
Idan kuma da Lambar waya ne, to ka tabbata lambar da kayi amfani da ita tana aiki, in ka sake lamba, to kayi maza ka sake lambarka a facebook: SETTINGS=>CONTACT INFORMATION=> a qasa zakaga wajen Number, baayan ka saka lambar, bayan ka saka Lambar, akwai Options da zasu baka, na wadanda kake so suga lambar, for more security ka zabi: ONLY ME!

**Sannan akwai wani tsari na TRUSTED CONTACTS: wannan tsari zai baka daamar zaban Abokanka na facebook da ka aminta dasu, in so samu ne, su zama suna kusa dakai, domin duk sanda Account dinka ya samu matsala, kuma ya zamana baka da email ko naka ya daina aiki, ko lambar da ka bude FB bata aiki, to ta hanyarsune zaka iya dawo da account dinka, kuma zaka iya saka daga mutum 1 har 10, don saka mutum: SETTINGS=>SECURITY=>TRUSTED-CO
NTACTS=>ENTER YOUR PASSWORD (anan zaka rubuta password dinka, domin FB su tabbatar da kaine ba wanine ya hau account din ba)=>ADD CONTACT (sai ka zabi wanda kake so)=>SAVE.

Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Mu hadu a kashi na 2

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post