Mai gidan Gilas Bai dace Yayi Wasan jifa ba!

Shek yakubu tare da mlm Sanusi


Ma'asumiya Nigeria news updates

Da sunan Allah mai rahama mai jinqai


Haqiqa harshe yana tattare da alkhairai da kuma hatsarin gaske da kan shafi rayuwa ta vangarori da dama, tasirinsa wurin qulla sharri ko alkhairi, yana kasancewa abisa tsarin da mai shi ya xora shi akai.

Kamar Idan mutum ya zavi harshensa a matsayin wani makami da zai qulla alkhairi da shi, yayi hani da sharri tare da horo da aikata alkhairi, za ka ga cewa a duk lokacin da ya furta magana babu suka ko zagin kowa a ciki sai dai Alkhairi. Za ka samu kowa yana maraba da kalamansa tare da jin daxin zancensa. Za ka ji mutane idan sun buxa baki suna ambaton alkhairi akansa.

Idan kuma mutum ya mayar da harshensa a matsayin wani makami da zai ci zarafi ko qulla sharri da shi ko tunzura wasu domin su aikata ba dai-dai ba, za ka ji cewa da ya buxa baki kalamansa ba na alkhairi ba ne. Za ka ji ya soki lamirin wani ko ya faxi aibi da sharrin wani, shi irin wannan mutun, mutanen kirki ba su maraba da kalamansa, za kaji mutane na faxin sharrukkansa, suna furta kalaman Allah wadai akansa. Allah ya kiyaye mu da kasancewa haka.

Shi dai laifi tudu ne kamar yadda Hausawa suka ce, mafi yawanci idan mutum na neman vata sunan wani mutum a idanun Al’umma, to lalle za ka samu kurakurai da yawa a cikin rayuwarshi waxanda shi ba ya ganin su, saboda haka yake ganin na mutane maimakon nashi. Amma mutane da yawa suna ganin waxancan kura-kuran, Shi yasa ake cewa ya take nashi ya hango na wasu.

https://maasumiya.blogspot.com/2018/06/quds-day-in-abuj-kaduna-other-towns-in.html?m=1

Irin waxannan mutane sune gwanaye a gurin cin zarafin mutane, sun qware sosai a gurin faxar abinda wani mutum yake aikatawa na zunubi a bayan idonsa. Duk wurin da suka zauna maganar guda ce, wane kaza yake aikatawa ko kuma wane ya aikata kaza, manufarsu xaya ce su vata sunansa ko su qas-qantar da darajarsa.
Idan kuma wani mutum ya yi rashin sa’a sirrinshi ya faxa hannun waxannan mutane, to sai dai fa idan an zo lafira Allah yayi mai hisabi da su. Domin za su bude sirrinsa ne ga faifai a duk inda suka samu kansu, za su sanar da kowa halin da yake ciki musamman idan sirrin nasa wanda zai iya zubar da qimar sa ne matuqa.

Yanzu idan na tambaye ka su waye ke aikata waxannan halaye me za ka ce? Kada ma tunaninka yaje nesa, dora lissafi daga kanka a matsayin mutum na biyu daga cikinsu domin ni ne na xaya, ko za ka ce min baka tava zaunawa aka yi firar wani da kai ba a lokacin da baya nan, kuma aka faxi ayukkanshi na sharri ko wani sirri nashi da ba zai so a faxi ba? Idan dai ma har ba kai ne ka bada labarin ba to tabbas ka saurara, kuma qila harda dariya ka yi. Wannan kuma don ba zarafin ka ne ake ci ba. Idan kai ne ake faxin aibinka ai ba za ka yi dariya ba.

A lokacin da duk kunnenka ya ji maka mutum xaya yana faxin aibinka, ko kuma yana cin zarafinka a gaban idonka, na tabbatar zai yi wuya ka mance da cewa an ci zarafinka a rana kaza. Amma kaima kanka idan da Allah zai baka ikon ka tuna da duk wata rana da ka yi maganar mutum a bayanshi, to da za ka san cewa akwai matsala a gabanka sosai. Amma ba za ka iya tunawa ba, saboda ba ka xauki abin komai ba.

Me ya sa za mu xore da aikata irin wannan mummunar xabi’a? Ashe za mu so duk wani laifi da muke aikatawa ya zama abin tattaunawar mutane a wurin firarsu? To mu me ya sa ba mu da wata fira ma’abuciya daxi face ta ambaton halayen Allah wadai na wasu mutane? Ko munsan cewa ba inda muke fira ba ne kawai wajen fira? Kuma muma muna da ayubba da yawa da za su iya zama abin firar wasu? To yayi kyau.

Idan mun faxi alkhairin wasu, muma sai Allah ya sa a faxi alkhairi akanmu. kuma ya rufa muna asiranmu ta yadda ba wanda zai sani face shi. Idan muka duqufa wajen biyar diddiqin laifin wasu, sai Allah ya bayyanar da laifukan da muke aikatawa a idanun al’umma. Qimar mu ta zube a duniya, Allah ya azabtar da mu a lafira akan laifukan da muka aikata. Allah ka tsare mu.
Kukan kurciya.........
ZA MU CI GABA

Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post