KOFAR TATTAUNAWA TSAKANIN IRAN DA AMURKA A BUDE TAKE,

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser kan’ani ya bayyana cewa, kofar tattaunawa ta diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka a bude take, kuma ana ci gaba da tattaunawa tsakaninsu amma ba kai tsaye ba, ta wasu hanyoyin diflomasiyya na masu shiga tsakani.


Nasser Kan’ani ya shaida a taron manema labarai na mako-mako a yau Litinin cewa, “Muna amfani da dukkan karfin diflomasiyya don tabbatar da hakkin kasa.”


Ya ce Iran tana aiwatar da manufofin ketare ta hanyar amfani da hankali da kuma cudanya da kasashe daban-daban, tare da kiyaye martabar kasa da al’umma.


Ya kara da cewa shigar da Iran kan hanyoyin da za a bi tare da kasashe daban-daban zai kara karfin kasar wajen yin shawarwarin diflomasiyya.


A halin yanzu Iran na cikin yanayi mai kyau kuma gwamnati mai zuwa za ta yi amfani da wadannan nasarori wajen cimma muradun kasa, in ji shi.


Kan’ani ya ce shigar al’ummar Iran masu daraja a zaben shugaban kasa da aka gudanar a baya-bayan nan wani sabon shafi ne a tarihin juyin juya halin Musulunci.


Kimanin kwanaki 50 bayan shahadar shugaba Ebrahim Raeisi, Iran ta yi nasarar gudanar da zaben shugaban kasa mai muhimmanci karo na 14, bisa karfafawa ta jagoran juyin juya halin Musulunci, da tsare-tsare na gwamnati mai ci, da rawar da ‘yan takara suka taka, da kuma fitowar dimbin jama’a.


Ya kara da cewa gudanar da zabuka biyu a cikin makwanni biyu a jere bayan shahadar Raeisi da yawan fitowar al’ummar Iran, sun tabbatar da cewa an kafa “dimokradiyyar addini” a kasar.


Ya jaddada cewa gwamnatin zababben shugaban kasar Masoud Pezeshkian za ta yi amfani da ikon Iran wajen cire takunkumin da aka kakabawa kasar ba bisa ka’ida ba.

@ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post