YADDA SHARI'AR ƳAN UWAN MU 60 TA GUDANA A YAU 1st DECEMBER 2023.

 


 A yau Alƙalin kotun bai zo kan lokaci ba, don haka an fara shari'ar ne misalin ƙarfe 4:00pm a maimakon 3:00pm da aka sanya tun jiya.


 A yau ƴan uwa 4 ne kawai suka bayar da shaidar su ta kariyar kai.


 Tun kafin shigowar Alƙalin, Shugaban gidan yarin na Kuje (Incharge) ya gana da Alƙalin, a inda ya roƙeshi da ya bayar da belin waɗannan ƴan uwa da yake tsare da su, duba da cewa su ɗin mutane ne masu son zaman lafiya, kuma tunda aka dawo da shi aiki a wannan gidan bai ji ba, kuma bai gani ba ko ya samu wani rahoto a rubuce cewa ga matsalar ƴan uwan nan.


 Sannan bayan kammala Shari'ar, ɗaya daga cikin ƴan Uwan ya tashi a gaban kotu ya ƙara roƙon Alƙalin da ya dubi yanayi na ƙunci da rashin lafiya da mafiya yawan ƴan uwan suke fama da shi ya basu beli, amma dai alƙalin ya turje a kan cewa wannan tuhume-tuhumen da ake ma ƴan uwan tuhume-tuhume ne masu girma da hatsarin gaske, kuma shi ne dalilin da ya sa ba zai basu beli ba, ya ce "amma dai zai yi bakin ƙoƙarin sa don ganin an kawo ƙarshen Shari'ar kafin ƙarewar sabuwar Shekarar 2024 da zamu shiga".


 Daga ƙarshe Alƙalin ya sanya ranekun 29 da kuma 30 ga watan Janairun Shekara mai zuwa don dawowa da ci gaban Shari'ar.


Kar mu yi sakacin yin addu'oi na musamman a kan waɗannan bayin Allah da ake ta take ma haƙƙi ba dare ba rana.


Ga Allah muke neman taimako.

Zaku iya samun ingantacciyar data ta kowane network akan sassauƙan farashi a FADAKDATA




1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post