RAHOTON YADDA SHARI'AR ƳAN UWA 60 TA GABATA YAU A ABUJA.Bayan zuwan Alƙali da lauyoyin dukkan ɓangarorin, an fara wannan Shari'a da misalin ƙarfe 1:30pm. 

Kamar yadda kowa ya sani cewa dama wannan zaman na yau ci gaba ne na kariyar kai da ƴan uwan suke yi wanda aka faro shi tun shekaru biyu da suka gabata.

A yau ƴan uwa shida ne suka gabatar da shaidar kariyar kai, maza uku tare da ƴan uwa mata uku.

Bayan kammala gabatar da shaidun kariyar kenan, sai ɗaya daga cikin ƴan uwan ya miƙe tsaye ya je gaban alƙali a madadin sauran ƴan uwa da ake tsare da su a gidan Yarin Kuje, ya gabatar ma alƙali wasu ƙorafe-ƙorafe da suke da su a kan wannan Shari'a da ta ɗauki dogon lokaci ana yin ta.

Daga cikin ƙorafe-ƙorafen akwai buƙatar da ƴan uwan suke da ita na cewa suna so a daina gabatar da shari'ar su a cikin gidan yari kamar yadda aka shafe shekaru ana yi, a maimakon haka a riƙa kai su kotu ne kamar yadda ake yi ma sauran tsararru yayin gudanar da shari'ar su.

A martanin Alƙalin Kotun, Alƙali Sulaiman Balgore ya ce "shi kan shi ba son zuwa Prison ɗin yake ba, saboda yana takuruwa sosai da hakan, to amma Hukumar gidan Yarin ce ta buƙaci da ya ci gaba da yin shari'ar a gidan yarin, sakamakon barazanar tsaro da suke fuskanta a duk lokacin da suka fito da ƴan uwan zuwa kotu" an dai yi doguwar taƙƙadama a kan wannan uzuri da Alƙali ya gabatar. 

Daga ƙarshe dai Alƙali ya saka gobe Juma'a ɗaya ga watan Disamba don a dawo a ci gaba da wannan Shari'a ɗin. A cewar sa hakan yana a matsayin tausayawar sa ne ga su ƴan uwan da ake tsare da su, da kuma fatan da yake da shi na ganin an kawo ƙarshen wannan zaune-zaune na Shari'a.

Har yanzu dai ana bukatar ƙarin addu'oin Mu'uminai, tare da ƙarin bayyana ma duniya kalar zaluncin da ake ma ƴan uwan mu.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah Ya gaggauta kawo mana dauki alfarmar Imam Ridha (a.s)

    ReplyDelete
Previous Post Next Post