WAZAN AURA DOMIN SAMAR DA ZURI'A TA GARI KASHI NA DAYA (1)

 



Ameenu Ak One Mairua 


Mafi yawancin lokuta Ana fara samun matsala tin lokacin da akazo neman auran.


Da yawa daga cikin ma'aurata ayayin da suka tashi yin aure, suna dauka cewar anayin aure ne Domi sharholiya tare da gamsar da juna. Batare da kallon aure a matsayin ibadaba.


Duk auran da aka Gina shi da wannan manufar dolene  a cigaba da samun matsalolin da daga karshe wannan matsalar itace zata cinye wannan auran.


Mafiya yawan mutane (maza da matan)  sukan yi aure ne batare da sanin haqqoqin auran ba. Shidai yaga budurwa ta iya shafa powder, Jan baki san Nan kuma ta kware wajan iya murda acuci shikenan sai aure.


Dan uwa kasani bance kada ka auri wadda ta iya shafa powder, Jan baki da acuciba, Amma kasani wadannan ba subane gane ma'aunin mace ta gariba.


Akwai qa'idojojin da shari'ar musulumci ta gindaya a lokacin neman aure, Wanda kuma kin binsu zai haifar da gagarumar matsala.


Na sani Manzan Allah (s)  yace  Ana iya auran mace saboda;

~ kyanta.

~Iliminta.

~nasabarta.

~Dukiyarta.

~Addininta.


Amma daga karshe yace na horeku da ku auri Mai addini.


Domin kuwa duk sauran zasu iya gushewa watarana, addinine kawai zai tabbata


Ya kamata Mai neman aure ya kalli tasirin uban yarinya agidansa ma'ana karfin fada agida, domin hakan zaiyi tasiri a zaman takewar auransu.


Kaguji auran diyar da mahaifiyarta kesawa ayi ko abari agida, domin zatayi dukkan Mai yiwuwa domin ganin yarta ta samu fiye da abin data samu (mallakar Mai gida).


Zanci gaba sati Mai zuwa Insha Allah 

08/Dec/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post