HARISAWAN AMIRUL-MUMININ ZONE, AZARE UNIT SUN SHIRYA PROGRAM DIN TUNAWA DA WAKI'AR BUHARI A GARIN AZARE.

 HARISAWAN AMIRUL-MUMININ ZONE, AZARE UNIT SUN SHIRYA PROGRAM DIN TUNAWA DA WAKI'AR BUHARI A GARIN AZARE. Harisawan Azare Unit karkarshin Jagorancin Shaikh Zakzaky (H) sun shirya program din tunawa da waki'ar Buhari wadda aka aukar ranar 12/12/ 2015 wadda #Buhari (L) bisa Umarninsa dana yaronsa #Elrufai (L) suka aiwatar a Garin Zaria dake Jihar Kaduna, yusuf tukur buratai ya jagoranta. 


Wannan Program an shirya shine a yau Lahadi inda aka fara tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka samu kansu a lokacin da Waki'ar ta afku, inda wasu wasu kuma na Gidan Shaikh Zakzaky (H) dake Gyallesu a lokacin waki'ar.


Bayan doguwar tattaunawar da akayi dasu kuma sun bayar da wani abu daga cikin yanayin da suka samu kansu, wanda duk wanda yaji irin wannan yanayin tabbas sai ya zubar da hawaye dan tsabar tausayawa, tare da kuma irin darussan da suka samu a wannan yanayin. 


Bayam an kammala tattaunawar dasu kuma sai shekh Aliyu dawud Abubakar wakilin yan uwa na garin Azare takaitaccen jawabi, daga nan kuma yanzu haka za a fita Muzahara. ©AZARE MEDIA FORUM

17/12/2023

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post