An yi kira da a hukunta makasan musulmi a Tudun Biri da nuna goyon baya ga Falasɗinawa

 


Ma'asuma Nigerian News Update

Da misalin ƙarfe 3:30pm na yammacin jiya Juma'a 8/12/2023.  Yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzkay (H), na garin Babban Rami suka fito kan titi. 


Domin nunawa goyon bayansu ga al'ummar kasar Falasɗinu. Akan halin da suke ciki, na kisan gilla da Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila take yi musu kimanin kwanaki sittin da ɗori (60).



Tare kuma da yin Allah wadai ga ta'addacin da Jami'an sojan saman Nigeriya suka yi. Kan al'umma musulmi maso yin Mauludin Manzon Allah (s), a garin Tudun Biri cikin karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.


Muzaharar wacce ta ƙunshi yan uwa maza da mata, yara da manya, da Dattijai. Duk domin bayyawa al'umma halin da yan uwa musulmin duniya suke ciki.



Daga kashe Malam Muhammad Tukur, wakilin yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzkay (H), na garin Babban Rami ya yi jawabin rufe. 


Inda yayi kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta daukan mataki akan wadanda suke yi kisan kiyashin ga masu taron Maulud a garin Tudun Biri. A daya ɓangaren kuma ya ja hankalin sauran al'ummar musulmi baki daya akan halinda al'umma kasar Falasɗinu suke ciki. Akan wajibi nuna goyon bayan a gare su.


Malam Tukur ya bayyana hakan yana daga cikin koyarwar da jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), yayi almajiran sa.


Daga kashe aka yi addu'a aka sallami al'umma. An yi lafiya an tashi lafiya.


Ga kadan daga hotunan da wakilin da ya aiko mana dasu.


Auwal M.  Tukur

9th December, 2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post