ABUBUWA 9 DAYA KAMATA MACE TA KIYAYE A LOKACIN AL'ADAR TA

 


 

Wanann bincike ne na wasu masana  da kuma likitoci. dangane da macen da take jinin al'ada yar uwa ya kamata ace kinsan dasu domin kiyi kokarin kaurace masu a yayin da kike jinin Al'ada..


GASU KAMAR HAKA..👇👇👇


1_ Kada kiyi amfani da ruwan kankara ko ruwan sanyi a lokacin da kike Al ada, saboda amfani da ruwan kankara yakansa jini ya daskare a mahaifa bazaitaba fita gabaki daya ba, wanda bayan shekaru 5 xuwa goma yakan kawo ciwon Daji na Mahaifa.


2_ A lokacin Al ada, kada ki sakawa kanki shamfo, kowacce kala saboda a wannan lokaci kofar gashinki a bude take, kuma shigar Shampo kofar gashi, yana kawo ciwon kai mai tsanani.


3_ A lokacin Al ada, kada ki ci Gurji ma ana Cucumber saboda akwai sinadarai a jikinta wanda zai hana jinin ya fita gabadaya, wanda daga karshe zai iya kawo ciwon Daji na mahaifa.


4_ A lokacin Al ada, koda wasa kada ki yarda a daki cikinki, kuma ki kiyaye duk wani abu da zai daki cikinki, saboda dukan ciki a wannan lokacin, zai yiwa mahaifa rauni wanda daga karshe zai iya zama ciwon Daji kuma yana kawo aman jini a lokaci guda.


5_ Kada kiyi amfani da gishiri mai yawa, amfani da gishiri mai yawa yana kawo yawan zubar da jini, kuma yakansa ruwa ya taru a Mahaifa.


6_ Kada kiyi amfani da kwakwa a lokacin Al ada saboda tana tsananta alamomi.


7_ A lokacin al ada, kada kiyi amfani da Barasa dukda bincike ya nuna tana rage radadi a lokacin Al ada, to akwai matsaloli da yawa da zai iya kawowa mace, idan tana amfani dashi.


8_ A lokacin Al ada, kada ki taba barin Pad sama da awa 3 zuwa 4 a jikinki koda jini baya zuwa Sosai.


9_ A lokacin Al ada, Tabar sigari dukkanninmu mun sani, tabar sigari yana da illa ga lafiyar jikinmu, bayan haka bincike ya nuna yawan amfani dashi a lokacin Al ada tana saka alamomi suyi tsanani.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post