WANNAN FA BA ADALCIBANE KUMA BA KOYARWAR ADDININ MUSLUNCI BANE

 


In annabi (S) ya kyautata wa Yahudu ko Nasara(Christians), sai ku ce kyawun halayenshi (S). In Nasara suka ziyarceshi (S) sai ku ce hatta su masun san Manzon Allah ne.

Lokacin da muminai sukayi hijira zuwa habasha kasar Kiristoci, kun yabi Sarki Najjashi, Kun yabi halifa Umar da ya ziyarci cocin Kiristoci a Kudus,
bayan Musulmi sun kwaci birnin daga hannun
Kiristoci.

Amma Kiristoci sun ziyarci Sheikh Zakzaky, kun tsinema Sheikh din Kuna Cin zarafinsa,

kun manta har masallacin Annabi
(S) Kiristocin Najran suka kawo mishi ziyara, kuma hatta malamanku ai su na zuwa su ziyarci Kiristoci. still bakwa cewa komai, kuma suma suna zuwa su
ziyarci malaman naku, kuma dai shima duk ba wani abu bane, ba kuga laifin hakan ba...

Sai don sun kaima malam Zakzaky ziyara ne Kai yake zama laifi aguriku?,

Sannan in makiya suka ce addininmu bana zaman lafiya bane, Sai ku dinga kumfar baki, 
Yanzu atunaninku hakan shine adalci..,

Ma'asumah Nigerian News Update
                Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post