AN BALLA RUMBUN ABINCIN DA GWAMNATI TA KILLACE ...



Wasu mutane a jihar Bayelsa da ke Najeriya sunfasa tare da wawushe rumbun tara hatsi da saurankayan abinci da gwamnatin jihar ta killace a birnin yenagoa domin raba wa jama’a da zummar rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa tun a 2022.Gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan abincin sun fara lalacewa.


An fasa rumbun ne da ke kan babbar hanyar Isaak Boro a yenagoa saboda irin tashin hankalin da al’umar ke ciki na hauhawar farashn kayayyakin masarufi wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da ya haddasa tsananin tsadar rayuwa.


Janye tallafin ne ya sa farashin man fetur ya yi tashin goron-zabi daga N190 zuwa 620 kan kowacce lita wanda hakan ya shafi farashin motocin sufuri da kayan abinci da sauransu.


Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa wadannan kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da ingancin da za a iya aci, domin sun lalace don haka duk wanda ya ci zai fuskanci matsala.


Da yake bayani kan mamayar da aka yi wa rumbun ajiyar, babban daraktan hukumar, Hon. Walamam Sam Igrubia, yace suna shirin tunkarar ambaliyar ruwa a bana, a lokacin da shugaban hukumar ya ziyarci wuraren, ya kuma tarar da sauran kayayyakin abinci, musamman shinkafa da gari wadanda ba su dace da ci ba.


Wannan shi ne karo na biyu, bayan wawason da jama'a sukayi a jihar Adamawa.

                 Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post