Sojoji sun kwato makudan kudade a hannun yan bindiga, tare da ceto mutum 9 da sukai garkuwa da su, bayan sojojin sun fatattaki yan bindigar


 BABBAR NASARA: Sojoji sun kwato makudan kudade a hannun yan bindiga, tare da ceto mutum 9 da sukai garkuwa da su, bayan sojojin sun fatattaki yan bindigar

Sojoji sun samu nasarar karbo mutane 9 'yan asalin jahar Sokoto da aka yi garkuwa dasu a cikin kauyen Gadar zaima ta jihar Zamfara. A lokacin bata wuta da akayi, Sojojin sun samu nasarar kàshe 'yan bindiga 10 tare da ràunata wasu da-dama.

Sojojin kuma sun kama mutane 2 cikin 'yan bindigar, tare da Bindigogi shida kirar AK-47, Bindiga 1 kirar 1PKT da kuma Magazine 5. Sauran su ne harsasai 7.62MM mai rawun 20, wayoyin hannu 3, Fanel din Sola 2, Keken Dunki (Tela) da Naira Miliyan 2,410,000.

'yan bindigar sun samu nasarar kàshe wata Mace cikin mutane tara da aka kwato a lokacin da suke bata kashi da Sojojin, kamar yadda Maibiredi TV ta rawaito mana. Allah ya kawo muna zaman Lafiya Mai dorewa

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post