Iran ta kaddamar da bikin sabon nau'in jirgin sama marar matuki mai suna MOHAJER-10


 Iran Ta Kera Jirgi Marar Matuki Mai Gudu Tamkar Haske

An kaddamar da sabon nau'in jirgin sama mara matuki na Iran mai suna MOHAJER-10 a wani bikin da aka gudanar yau Talata, wanda ya samu halartar shugaban kasa, Ibrahim Raisi da ministan tsaro da manyan kwamandojin soji. A cewar wakilin tsaro na IRNA, jirgin mara matuki mai suna "Mohajer-10", yana tafiya kamar haske. 

Mohajer-10 yana da matsakaicin shan man fetur na lita 450 da matsakaicin nauyin kilo 300. Jirgin mara matuki yana daukar alburusai da bama-bamai iri-iri. Haka kuma yana da tsarin tattara bayanan sirri. Wani masanin tsaro ya bayyana cewa kera wannan jirgin ba karamin ci gaba Iran ta samu ba. Ya yi hasashen cewa ba da jimawa ba kasashen duniya za su fara rubibin mallakar sa.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post