‘Abin da ya hana a magance karancin lantarki a Najeriya


 Najeriya ta dade tana fuskantar matsalar lantarki


13 Yuli 2022

Injiniya Sani Bala Tsanyawa, dan kwamitin wutar lantarki ne a majalisar Wakilan Nigeria, kuma tsohon jam'in hukumar samar da wutar lantarki ta kasa , NEPA ya ce matsala ce ta siyasa ta hana a samar da isasshen karfin wutar lantarki a kasar. 


 Ya ce a shekara ta 2005 lokacin da Olesugun Obasanjo yake mulkin Najeriya an cire tsabar kudi daga asusun rarar man fetur na Najeriya har dala biliyan 2.5 domin kai wa bangaren na wutar lantarki agajin gaggawa. Asusun dai shi ne ake ajiye kudade wadanda dukkanin bangarorin kasar ke da hakki a cikinsa.Daga nan ne aka kirkiri kamfanin samar da wutar lantarki na Niger Delta Power Company wanda aka ba shi aikin samar da tashoshin wutar lantarki masu aiki da Gas a kudancin Najeriya.A karkashin kamfanin Niger Delta Power Company, a cewarsa aka kafa wani bangare da ake kira Nigeria Integrated Power Company. An kirkiri shirin ne domin ya kafa tashoshin samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin gas a kudanci, da kuma kafa tashoshin samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa a arewacin kasar.


A wancan lokacin, a cewar Injiniya Tsanyawa, an kafa tashoshin samar da lantarki masu amfani da gas da dama a jihohin kudancin kasar, amma daga baya sai aka yi watsi da aikin kafa tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da karfin ruwa a Arewa. Ya kara da cewa yarjejeniyar ita ce za a sayar da tashoshin samar da wutar lantarkin masu amfani da gas ne ga kamfanoni masu zaman kansu, sai a yi amfani da kudaden wajen kafa tashoshin samar da wutar lantarki a bangaren arewa. Kuma a cewar sa daya daga cikin tashoshin da za a gina a Arewa har da ta Mambila, wadda aka kiyasta za ta samar da karfin wutar lantarki megawatt dubu uku.Sai dai ya ce hatta tashoshin samar da lantarkin da aka kafa a kudu, na yi watsi da su saboda rashin kyakkyawan tsari, inda wasu daga cikin su sai da suka kwashe shekara 10 ba tare da an yi amfani da su ba. Wasunsu saboda ba a já masu bututun da zai kai mas ugas ba, wasu kuma na yi su ba tare da hada su da layin rarraba wutar lantarki na kasa ba.


Ya kuma kara tabbatar da cewa har yanzu babu wani aiki da aka yi a tashar wutar lantarki ta Mambila wanda ya wuce kokarin biyan mazauna yankin diyya domin su tashi daga wurin da aka shirya samar da madatsar ruwan.

Sai dai ya ce aikin da gwamnatin Najeriya ke yi a yanzu na shimfida bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kano zai iya taimakawa wajen samar da gas din da za a kafa tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da gas a arewacin kasar.


Ya ce matsalar da ake fuskanta ta katsewar wutar lantarki ya samo asali ne daga rashin isassahen ruwan da ke motsa injina a tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da ruwa a arewacin kasar, musamman a lokutan da ba na damina ba. A cewarsa samar da tashoshi masu amfani da gas shi ne zai magance matsalar. 

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post