LOKUTA BIYAR NA TSANANI GA IYALAN IMAM HUSSAIN (AS)....Na Farko; Daran fitar Imam Hussaini daga Madina, Iyalan sa sun fita cikin tsoro da jinkirin abinda zai faru da su a Karbala, domin Imam Hussaini be rufe musu komi ba, yace musu za'a kashe shi a gaban su, su kuma za'a kama su a matsayin bayi.


Na Biyu; Daran da Imam Hussain suka nusa shi da Hurr, daga muhallin da ya tare su a matakin farko na niyar su ta zuwa Kufa, zuwa filin Karbala, saboda Iyalan Imam din sun san za'a je ga muhallin da za'a kashe mazajen su, su kuma za'a kama su a matsayin bayi.


Na Uku; Kasancewarsu a filin Karbala da sunan ribar yaƙi zuwa Kufa, ana tafe ana dariya ana dukan su, tare da hakan suna ganin kan Hujjar Allah Imam Hussain tsire akan mashi da sauran Sahabban sa.


Na Hudu; Shigar su fadar Ibn Ziyad.


Na Biyar; Shigar su Sham (Syria) da kuma komawar su Madina, wadda har Sayyida Zainab ta rera wata kasida dab da Shigar su Madinan.


Ga baitin kamar haka...


Madinar Kakanmu bata tarbemu ba 🥺.


Domin a ribatattu yaki da Bakinciki muka dawo 😥.


Mun Fita daga cikin ki tare da Iyalan mu 👨‍👩‍👦‍👦.


Mun dawo ba tare da Mazajen mu ko Yaranmu ba 😭.


Amincin Allah ya tabbata gare ka ya Baban Abdullahi Hussain ɗan Ali (As).


Daga Littafin Nahzatul Hussainiyyah. 


Mai Nakaltowa; Muhd Bala Afuwa 

By Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News Update Mnnu//Ng0027


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post