KO ASADUSSUNNAH ZAI FADA MANA BARNAR DA MALAM ZAKZAKY HAFIZAHULLAH YAYI.......???

 


Menene barna a karatu da mahangar Asadussunnah? 

Shin Asadussunnah yana nufin barna irin wacce Malaman addini suke yi na raba kan Musulmai da cusa gaba a tsakanin al'umma ko kuwa barna irin ta biyayya ga fasikai, fajirai da azzalumai ko kuwa barna irin wacce Almajiransu suke yi a Arewa maso Gabashin Nigeria da sunan addinin Musulunci? 

Ko dai Asadussunnah yana nufin barna irin wacce Almajiransu suke yi a Nigeria idan rigingimun  addini ko Siyasa sun tashi da sunan Jihadi? 

Ko kuwa barna irin wacce Almajiransu suke yi a kasashen Larabawa da wasu kasashen Afirka da sunan Jihadi? 

Ko Asadussunnah yana da hujjojin da suka fito a rubuce daga Jami'an tsaron Nigeria ko kotunan Nigeria wanda aka taba samun wani daga cikin Almajiran Malam Zakzaky Hafizahullah ya kai hari a wani Masallaci, Coci, kasuwa ko unguwanni da sunan addinin Musulunci?

Ko Asadussunnah yana da rubutaccen rahoton kashe mutane da kona dukiyarsu daga Almajiran Malam Zakzaky(H)?

Shin Asadussunnah ya taba binciken record din activities na Malam Zakzaky(H) a barikokin Sojoji, ''Yansanda, NIA, DSS da sauran Jami'an tsaron Nigeria ne ya ga ta'addanci da barnarsa? 

Na maka Wadannan tambayoyin ne Saboda kace idan aka ba wa Rabi Salisu kwamishinar Women affairs ta Jihar Kaduna barnar da zata yi muku ko Zakzaky bai yi ba, ko zaka fada mana barnar da yayi? 

Ko dai kisan ta'addancin da Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yiwa 'Ya'yansa uku da Almajiransa talatin da daya ne barnar Zakzaky?

Ko kuwa kisan ta'addancin da Gwamnatin Buhari da ta El-rufa'i suka yiwa 'Ya'yansa Hudu da Almajiransa sama da dubu da raunata shi da Matarsa da kulle su tsawon shekaru da rusa Gidansa da komai nasa ne barnar? 

Ko kuwa caje aljifan gawarwakin Almajiransa da Almajiranku suka yi da yanke yatsa domin cire zobe ne barnar? 

Ina fatan Asadussunnah zai cire hasada da kiyayya da gaba da Shi'a yayi adalci ga kowa har wadanda ba Addininsu dayaba... 

Umar Hassan Gololo 

Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News Update Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post