DAKA KARBALA: ƊAGA TUTAR ‘LABBAIKA YA HUSSAIN’ YA ZO DA SABON SALO.
Da yammacin nan na yau Talata 29/12/144 (18/07/2023) daga birnin Karbala Iraq, a haramin Abu Abdullahil Hussain (A.S) da Haramin Abdul Fadhlul Abbas, an ɗora tutar Labbaika Ya Hussain a saman Qubbar haramomin.


A lokacin ɗora tutar dai an rika ambatar taken “LABBAIKA YA HUSSAIN” da sautin da duk illahirin wajan abinda ka ke ji kenan. Dubunnan al’umma ne suka halarci ɗaga tutar sai dai wani abu da ya ɗauki hankali shi ne ɗaga tutar ya zo da wani sabon salo domin a yayin ɗaga ta dubunnan al’umma ne suka daga Al-Qur'ani mai girma sama domin nuna soyayya da kishin littafin mai tsarki gami da girmamawa kan cin zarafinshi da ƙona shi da kasar Sweeden ta yi.


Ɗaga tutar dai wanda duk shekara an saba yinsa, wani alami ne da ke nuna cewa watan juyayin Ashura ya kama, wato watan da aka kashe jikan Annabi Imam Husaini (A.S) a filin Karbala a shekara ta 61 bayan Hijirar Manzon Allah (S). Taken Ashurar bana shi ne ‘Wafa’un Lil-Hussain’ wato (Cika Al-ƙawari ga Imam Hussain).


Sai dai a irakin alamu na nuna wata zai cika Talatin, wanda ake sa ran ranar Alhamis ya zama 1 ga Almuharram.

—Bin Yaqoub Katsina


#Ashura1445_2023

#وفاء_للحسين


 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post