Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Sun karbi Ababen Hawansu Da Hukuma Tarike Kusan Shekaru 8.

 


Kamar yadda aka ayyana yau Asabar 1 ga watan Aprilu 2023 ne yan uwa musulmai almajiran Sheikh Zakzaky zasu karbi ababan hawansu motoci mashina Keke Napep. Wanda jami'an tsaro suka  kwashe wani ba 'adi agidan sheikh Zakzaky gyallesu ,  dakuma Husainiyya Bakiyyatullah a shekarar 2015 bayan kisan dubban yan uwan a zariya. 


Yan uwan dai sun hallara police station dake MTD Zariya  inda bayan tantacewa  kowa yafara daukan nashi. Saidai yan uwan sunyi korafin dayawansu sun rasa wasu sassan na Motocin nasu cikin abubuwan dasuka bata harda inji nawasu motocin.Ababan hawan dai da aka bayar yau motoci guda 67 mashina karfe karfe guda 10 , Keke Nafef guda 3. sa'ilin da ninkin adadin abin hawan anyi wasoso .wasu kuma  ankona , wasuma agaban masushi  ake saidawa .


Ayau da'ake karban ababan hawan , dayawa daga cikin masushi suna cikin wanda aka kashe agyallesu gidan sheikh Zakzaky ko kuma Husainiyyan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post