Shierk Ibraheem Zakzaky (h) Ya Mika Sakon Ta'aziyyar Shi ga Allama Sayyid Haidar Hakim, da daukicin Iyalan Sayyid Hakim da sauran masoya..! Sakon Ta'aziyya


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ


يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ * ارْجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً * فَادْخُلِي فِي عِبَادِي * وَادْخُلِي جَنَّتِي


Cikin bakin ciki da alhini muka samu labarin rasuwar Allama Sayyid Sadik Hakim dan gidan Shahidi Ayatullah Sayyid Mohammad Baqir Hakim daga iyalan gidan ilmi da gwagwarmaya da sadaukarwa.


Bisa wannan babban rashi Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ke mika sakon ta'aziyya ga Allama Sayyid Haidar Hakim, Sayyid Jafar Hakim, Sayyid Ammar Hakim da daukicin Iyalan Sayyid Hakim da sauran masoya. 


Muna  rokon Allah Madaukakin Sarki da ya saukar da rahamarsa ga wannan marigayin mai daraja, ya sanya Aljanna ta zamanto ita ce makomarsa ta har abada, sannan kuma ya ba wa iyalansa da kuma masoyansa hakuri da juriyar wannan rashi. 


Inna lillah wa inna ilaihi raji’un!


#Al-fatiha ma'as salawat

@Szakzakyoffice   

31/03/2023

Ramadan 9 1444 AH

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post