SHIN WADANNE HANYOYI YAN MATA DA ZAWARA ZA SU BI DAN KARE KANSU DAGA SAMARI YAN INA ZAMU HADU?

 


_Tare da ni Habib Nasrallah_


A ko da yaushe yan mata da zawarawa suna bukatar yin aure amman babban tashin hankalin nasu, gasamari iya samari na tururuwar zuwa amman sai dai kash kaso 98% cikin dari samarine yan ina zamu hadu? Tare da cewar wanna jimla da ta yawaita a bakunan yan mata da zawarawa, na nuna cewar akwai ayar tambaya. Abin la'akari anan shine, menene ke jawowa yan mata da zawarawa samarin yan ina zamu hadu?


Kaso 99% cikin dari yan mata da zawarawa suke jawowa kansu samarin yan ina zamu hadu, babu yadda za'ayi mace da akasanta da daraja da kima da mutumci idan har ta watsar da wadannan abubuwa babu yadda za'ayi bazata hadu da samari yan ina zamu hadu. Za kaji cewar yan mata da zawarawa su na cewa ina son nayi aure amman har yanzu babu wani tsayayya, ga samarin amman babu wani tsayayye sai dai samari yan rage dare. Abin tambaya anan shine wadanne abubuwane suke jawowa yan mata da zawarawa samarin yan ina zamu hadu? San nan waddanne hanyoyi yan mata zasubi dan kare kansu daga samarin yan ina zamu hadu?


 

*1. Dolane ki zamo mace me cikakkyar tarbiya, kamin kai, nutsuwa, watsi da kalmomin ashsha, kizamo ma'abociyar addini idan ke musulmace d.s*


*2. Dolane mace ta zamo me shiga ta kamala, karki kuskura kibi dabiar wasu shiga ta suttura da kike gani a fina-finai, sai mage tasamu tarbiya sannan zata tarbiyantar da 'ya yanta, haka kuma Hausawa na cewa, danyan kasko ba yakai ruwan wanka bandaki. Sabo da haka dolane ki kare kanki daga shigar daba tadaceba da addini da al'ada*


*3. Wajibini mace ta zamo me karanta magana da yawaita dariya a gaban maza, ko da acikin yan uwanki mata yawaita dariya ta na da illa tana gusar da imani, tana kuma kawo raini tsakanin ki da kawayanki.*


*4. Haka kuma dolane mace tazamo me sassauta muryarta kata kasance ta na daga muryarta ko da ko a gidan kune, domin idan kikasaba ko da a gidane to a wajema zaki daga murya baki sani ba dole mata sukula da wannan*


*5. Dolene mace ta guji kwadayin abin hannu daga samari, ki guji roko ko saurin karba abin saurayi ya baki, ki nuna masa cewar abinsa ko dukiyar sa bata da mahalli a zuciyar ki, ko da ko kin kasance mabukaciya indai har kina san kare kanki da mutuncin ki yawajaba ki nuna masa haka*


*6. Ki guji kawowa saurayi kukan abin dake da minki ko ya faru a gidan ku ko danginku wanda kika tabbatar da cewar zai zubar da mutunciki da kimar idan bata kama doleba ko ababin neman shawara*


*7. Wajibine kisan kanki, kisan wacece ke, wacce daraja Allah yayimiki a matsayin ki na ya mace, kisan da cewar idan kika zubar da mutunciki da kimarki kika taketa ki ka watsar da ita kika tozarta kanki ta hanyar son abun duniya dabawar da kanki da samarin yan ina zamu hadu ki tabbatar da cewar kin yi hannun riga da samari nagari, sai kin yi sa'ar gaske kisamu wanda zai rufa miki asiri, ko da ya aureki taciki na ciki tabaka na baka, duk irin soyayyar da ya ke miki, namiji yana da wannan dabiar*


*8. Ki guji duk wata kwalliya da kikasan zata jawomiki samarin yan ina zamu hadu? A lokacin da kika zubar da mutunciki da kimar ki, lokacin da zai zage yayi auransa ke kina nan kina jiran gawan shanu, su kuma na kirki da sunzo sun fara bincike za'a kyasamu wannan fa da akwai magana karshe ya kama gabansa, sai dai kiga taganin tururuwan samari yan ina zamu hadu*


*9. Wajibine mace ta nisanci duk wasu kawaye masu kiran samari yan ina zamu hadu, ta hanyar shigarsu da aikin su. Dolane ta yi mu'amala da kawaye masu kamun kai idan ta na bukatar kare kanta daga samarin yan ina zamu hadu*


*10. Ki guji duk wani saurayi da ya zai daukeki ku tafi wajan siyayya ko yawan shakatawa, ko da ko an samuku rana madamar baki zama matarsaba da kinyi haka kin nuna cewar bakisan kankiba bakisan wacece keba yau da gobe zai kaiki ya baroki yayi miki babban taban da bazaki manta da shiba*


*11. Wajibine mace ta kula da kalmomi da zata rinka furtawa a ayin da ke zantawa da saurayinta. Kada idan namiji ya nunamiki shifa bashi da kunya kema kinuna masa baki da kunya. Kada ki dauki hoto batare da cikakkyar sutura hijabi ko mayafi ba ki turawa duniya a social media hakan zai jawomiki samarin yan ina zamu hadu. kada idan yayi miki zancen banza ko ta text ko ta waya, ki yi dariya ko kinuna rashin da muwarki, karki ki ce zakibi wankan samari a zamo mudubinki wajan zabar mijin aure, yi kokari ki duba ma'abocin addini, idan ke ma'abociyar san wanka ne, zaki iya gyara abin ki ta cikin hikima da dabara, yafi ki dauko wanda zai cutar da rayiwar ki ya tafi yabar ki ke da iyayan ki cikin kunya da rufa-rufa, haka kuma duk irin san da kike masa ki dauka cewar ada bakisan shi ba, haka kuma idan kin rabu dashi zaki samu wanda yafishi, domin Allah ne ke bayar da miji ba yin kanki bane ko da barar ki, bakya ganin wasu matan Allah yayi musu sura amman babu mazan auran? Suna zaune a gida tun basa da muwa har abin na damunsu, amman wacce bata kaisu kyauba ta samu mijin aure?*


Abu na karshe


*12. Ka da ki zamo mace me yaudara maganar gaskiya shine akwai namijin da ba'a yaudara sai ya dauki fansa ta ko wacce hanya, idan bakya sanshi hatta abin hannunsa ki gujeshi, idan kuwa ba hakaba za kici karo Da samari yan ina zamu hadu. Haka kuma dolene ki yawaita addua da samun miji nagari, karki yi zatan zaki watsar da kanki daga bisani kiyi zatan zaki sami mijin aure na gari a'a da wahalar gaske, ko da ya aureki kitabbatar da cewar ke ba me darajace a gunsaba, yana kallanki a matsayin wanda ya rufamiki asiri.*


 Sabo da haka wajibine yan mata da zawarawa ayi taka tsantsan. Haka kuma wajibine mu maza mu kula, karkaje ka bata yar wani kayi zatan baza abata nakaba, na tabbatar da cewar bazakaso a lalata kanwarka ba ko yayarka to me yasa kai zakaje kabata kanwar wani ko yayyar wani? A matsayinka na namiji na tabbatar da cewar baza taba yarda ka auri lalatacciyaba ka na burin ka auri gyararriya idan ko kanasan haka to karka lalata yar wasu sai ka auri gyararriya, idanma ka auri gyararriya to kajira kaga yayan da zaka haifa.


Akarshe ina adduar Allah yashiryar da mu, matan da ke neman maza nagari Allah yabasu a matsayin mazajen aure na har abada, me ra'ayin mace daya tak daga ita ba kari, domin nasan da cewar mata da yawa basasan abokon zama (kishiya) to haka za ayi hakuri akarba ko ba komai bazakiso ace mijinki yana fasadi a waje da wasu matan ba, gwara ya auro kinga kin kareshi daga fadawa kwazazzabon wuta.


Wassalamu... Alaikum warahmatullah ni ne naku har kulum.

Habib Nasrallah.


*©Habib Nasrallah*


Email:habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post