GAREMU ƳAN SHI'A !!!:- Babban Qalubale Mai Hadarin Gaske Dake Kewaye Damu A Halin Yanzu..!!
Wajibi ne akanmu mabiya Ahlul baiti (Ƴan Shi'a) mu kasance cikin takatsan-tsan game da sha'anin Aƙida da manhajinmu da Ahlul baiti (a.s) suka shimfiɗa mana shi kuma suke so mu Addinantu dashi .

Babu shakka soyayyar Ahlul baiti (a.s) wani rukuni daga cikin rukunan Addini, haka nan yabonsu wani babban arziƙi ne a Duniya da lahira , amma hakan baya nufin mu yaudari kanmu ko mu ruɗu kai tsaye da duk wata da'awa da yazo mana da sunan soyayya ko yabon Ahlul baiti (a.s) , bayan kuma raunatawa da gurɓata tattaciyar Aƙidarmu take mun sani ko bamu sani ba .


Don mutum yayi da'awar soyayyar Ahlul baiti ko yayi yabonsu hakan baya nufin ya zama ɗan Shi'a cikakke , ko ya zama malaminmu a Aƙida da zai koya mana so ko yanda ake bin Ahlul baiti (a.s) , kamar yanda ba don kawai mutum ya fahimci Shi'anci shikkenan ya zama Malami a Shi'a ba , a'a ! Lallai Shi'anci yana da tsari da Ladabi (Displine) da ake karantarsa a gaban Malaman Shi'a , amma duk ilmin mutum a inda ya baro kafin ya fahimci Shi'a hakan baya nufin ya zama Malami a Shi'a ba tare da yayi karatun Shi'anci ba .


Maganar gaskiya abun farin ciki ke irin yanda ake samun wasu sautika mabanbanta daga ko ina suna rera yabon Ahlul baiti (a.s) tare da da'awar ƙaunarsu da ɗaukaka ambatonsu , wannan yana ƙara nuna mana cewa lallai wannan zamanin Ahlul baitin ne , sai dai ba'a nan gizon ke saƙa ba ! Domin magana ta gaskiya dayawan wasu ƙasidu da ake yaɗawa da sunan yabon Ahlul Baiti (a.s) ko ɗaukaka ambatonsu , cike suke da kura-kurai a matakin Aƙida da Ladabi , ta yanda ake wuce gona da iri da kaucewa ingantattun Aƙidun da Ahlul baitin suke kansu , ba ta ya yadda za'a yi mutum ya dinga faɗar miyagun Aƙidun da Ahlul baiti suka tafi da rayuwarsu wajen yaƙarsu kuma wai da sunan yabonsu ! Haka a matakin ladabi ana amfani da kalmomi marasa kan gado da lissafi da sunan yabonsu , bayan kuma su suna da tsari da ladubba da suka bamu idan zamu bayyana soyayyarmu garesu ko mu yabesu , ina ƙara maimaitawa bance duka ba.... amma wallahi dayawan ƙasidun da ake da sunan yabon Ahlul baiti (a.s) in mutum bai hankali ba za su jefashi a rijiyar halaka bai sani ba , ba ta yadda za'a yi Ahlul baiti su yarda da ƙasidu na keta haƙƙin Allah da Shari'a da sunan yabonsu , ya zama wajibi muyi hankali .


Amma abun takaici mu (Ƴan Shi'a) sau dayawa bama hankalta mun rafkana ga barin gane hakan , ban sani ba ko shauƙi ne ko rawar jiki da ƙarancin wayewa suka sa bama yin hattara sosai , sai ya zama guguwa dayawa na ƙoƙarin kaɗamu daga duk inda ta taso cikin sauƙi , wallahi dayawan wasu maslaha irin ta mawaƙi kamar son shahara ke sa su yin yabon , shi yasa suke saka siyasa da dabaru ko a cikin wasu baitukan yabon suna yin shaguɓen cin fuska garemu (Mu ƴan Shi'ar) amma bama iya ganewa , sai ya zama suna ƙokarin ruɗarmu su samu abinda suke so kuma suna nunawa wasu su ba wai Shi'a suke ba akwai abinda ya kawosu , wasu kuma da gaske har ga Allah yabon da ƙaunar ce a gabansu kawai zamiya ce suka samu saboda ƙarancin saninsu ko abinda yayi kama da haka .

An ruwaito daga Imam Ali (a.s) yana cewa : Kar ku ƙetare damu matakin bayi ga Allah , ku faɗi abinda kuke so akanmu amma ba za ku iya kaiwa mauƙurarmu ba , kuma na haneku da wuce gona da iri kamar wuce gona da irin Nasara (Kiristoci) , lallai babu Ni babu masu wuce gona da iri , Aɗɗabrasi ne ya ruwaito shi a cikin Al-ihtijaj ɗinshi .


Akwai wasu tarin ruwayoyin da Ahlul baiti (a.s) suke karantar damu ladabin yabonsu da faɗar matsayinsu don nuna soyayya da ƙauna , wanda suke jadadda mana mu kiyayi wuce gona da iri (Guluwi) a kan sha'aninsu sannan kuma mu lazimci riƙo da karantarwarsu a duk abinda za mu faɗa .


Don haka duk mai son ya yabi Ahlul baiti (a.s) ko ya saurari yabonsu , ko ya faɗi wani abu daga matsayinsu ko yayi musu kirarin ban girma , dole ya zama ya kiyaye wasu abubuwa masu muhimmanci daga ciki :


1. Kar ya zama abun da zai yi ko ya faɗa ya saɓawa tabbatacciyar Aƙidar da Ahlul Baiti (a.s) suka koyar .


2. Kar ya zama ya saɓawa karantarwarsu a cikin abinda zai faɗa da kowacce irin manufa .


3. Ya zamanto yana tuntuɓar waɗanda yasan sun fishi sani da haske a wannan fage da yake sukuwa a cikinsa , domin wuri ne mai tsarki da santsi in ba'a yi da gaske ba sai a rasa Duniyar da Lahirar da rabin kalma ina aka furta , garin neman gira a rasa ido.


4. Ya zama wajibi a komawa rayuwar magabatan Sha'iran da suka yabi Ahlul baiti (a.s) tun a rayuwar Ahlul baitin , suka samu karɓuwa da gam da katar har tashin alƙiyama , ta yanda ya zama suna karanta Ƙasidunsu a gaban Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s) kuma suka karɓa suka yarda da baitukansu , Irinsu Hassan Bin Thabit a zamanin Annabi (saww) , Kumaitul Azdiy , Di'ibilul Khuza'iy ,Sayyid Himyariy ,  da wasunsu , mutum ya dinga bibiyar ƙasidunsu yaga yanda suke yabon Ahlul baiti (a.s) a yanayin farin ciki da juyayi don ya ɗau samfuri daga magabata , dama wasu da suka zo ba'a zamanin Ai'mma ba , irinsu Al-khulai'iy d.s.


5. Yana da kyau ya zama yana da ilmi akan tarihinsu da rayuwarsu da karantarwarsu kafin yace komai akansu , in ba haka ba duk abinda zai faɗa jahilci ne ko ganganci ne a haƙƙinsu .

Amma wallahi in mutum bai hankali ba game da sha'anin yabo da ƙaunar Ahlul baiti (a.s) zai ɓata dubu 1000 bai gyara ɗaya ba , Allah ya kiyashemu ! 


Wallahi ba wai ina sukar masu tasawa da rera yabon Ahlul baiti (a.s) bane a ƴan shekarun nan , nakanji daɗin yadda ake ta samun cigaba , to amma fa hakan baya hana in faɗi gaskiya kuma zalunci ne yin shiru akan irin wannan al'amari , ga kuma barazana ga Aƙidarmu da Ahlul baitin suka ɗora mu akanta , in muka yi shiru mu zamu cutu musamman nan gaba .

Kuma ba ina tubumarsu da suna yi da gangan bane sam , nasan mafi yawansu rashin sani da ƙarancin ilmi ne ya kaisu ga hakan - kuma nima ban wuce na samu zamiya a cikin hakan ba -  to amma abun ne ya fara yawa dayawan ƴan uwa bama lura , ya zama wajibi mu farka ! Kar mu ruɗu da sunan yabo da soyayya ! Dole mu kula da Aƙidarmu da manhajinmu kar mu rasasu .


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️Abu HaidarAl-Abdul Faneey Al-kanaweey 


https://t.me/tafarkintsiratv


16 / Ramadhan/ 1444H - 7 /4 / 2023 Miladiyya.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

 1. Salam Alaikum
  Wannan jawabi da Abu Haidar yayi gameda matsalolinda ke tasowa a cikin yadda wasu mawaka suke wuce waje suke baiwa Ahlilbaiti A. S siffofi na Ubangiji duk da cewa su A'immatu Ahlilbaiti sunyi hani ga hakan, gaskiya abin haka yake kuma lallai yanada hadari ga sahihiyar karantatwa ta Ahlilbaiti akan abinda ya shafi akida.
  Daga cikin dalilanda ya sanya hakan yana faruwa shine kasancewar da yawa daga cikin masu irin wannan kura kurai kafin su shigo ko su fuskanto zuwa ga irin wannan yabo da sukeyi dama acan suna cikin darikun sufayene wanda babu shakka akwai ababe a cikin dariku na jazba da falsafa wanda ya sabawa ainihin karantatwa ta Ameerul Momina Aliyu Bn Abi Talib da sauran Imamai na Ahlilbaiti A. S to amma saboda su wadannan mawakan basusan matsayar Annabi da Ahlilbaiti akan irin wadannan maganganuba sai su rinka furtasu da sunan suna yabon Ahlilbaiti A. s.
  Kalmomi irin na "yan hakika da kalmomi da ake baiwa Aimmatu Ahlilbaiti siffofin rububiyya ko Uluhiyya ta hakika abune wanda Aliyu Bn Abi Talib A. S yayi hani a garesu kuma saboda hakane a kasashe inda karantarwa da soyaiya da biyaiya da cikakiyar biyaiya ga Ahlilbaiti suka samu gindin zama shekaru daruruwa zuwa dubu irinsu Iraq, Iran, Lebanon, Pakistan, Kuwait, Saudi Arabia, Dubai, Bahrain da sauransu wannan irin halaiyar ba karbabiya bace ko kadan.
  Babu shakka akwai aiki a gaba ga masu son ganin abin mazhabar Ahlilbaiti kamar yadda take, cewa dolene su mike tsaye wajen karantarda wannan mazhaba mai tsarki kamar yadda take a ainihi.
  Wassalm Alaikum

  Abbas JG

  ReplyDelete
Previous Post Next Post