SHARADIN DAKE WAJABTA QASARUN SALLAH SHI KE WAJABTA SHAN RUWA YAYIN TAFIYA !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ADDINI BA RA'AYI KO BIN SON ZUCIYA BANE 


Addinin muslimci wanda Annabi Muhammad (S. A. W. W) yazo mana dashi kuma ya karantar damu yadda ake yinsa bai bar mana wani abu cikin dahu ba face sai da ya bayyanar mana dashi. 


Idan kaga mutum na aikata wani sabanin abinda Annabi (S. A. W. W) ya koyar damu zai iya zama rashin sani ko kuma bin son zuciya. Kuma wadannan abubuwa biyu su ke halakar da al'umma, wato jahilci da bin son zuciya. 


Babu wani abu dake janyo yin qasarun sallah face shine dalili ko hujja ko kuma sharadi na ajiye azumi yayin tafiya. Saboda haka ba a rabe tsakanin wadannan abubuwa biyu. A duk lokacin da kaga wani abu ya faru wanda ya janyo rage sallah (Qasaru), do abinda ya zama wajibinka a gurin shine ka ajiye azuminka. 


Wannan dalili na cikin Qur'ani da Hadisan Ma'aiki (S. A. W. W) kamar yadda za mu iya kawo misalai dasu. 


Allah (T) na cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


" أَيَّامًا مَعْدُودَاتٍ فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَنْ تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ وَأَنْ تَصُومُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ." (184)}


" KWANUKA NE QIDAYAYYU, WANDA YA KASANCE BA SHI DA LAFIYA DAGA CIKINKU KO KUMA YANA HALIN TAFIYA SAI YA RAMA SHI  A WASU KWANUKA NA DABAM. GA KUMA WANDA (azumin) KE WAHALAR DASHI (saboda wata jinya ko kuma tsufa) SAI YA CIYAR DA MISKINAI (a matsayin fansa), WANDA YAYI TADAWWI'I NA ALKHAIRI (qari kan abinda zai isa ciyar da miskini) HAKAN YA FI ALKHAIRI GARE SHI. AMMA DA ZA KUYI AZUMIN (komai wahalarsa) SHINE MAFI ALKHAIRI GARE KU IN DA KUN KASANCE KUNA SANI. "


(BAQARA, AYA TA 184)


Abinda muku son fitarwa daga cikin wannan aya shine umarnin Allah na cewa a ajiye azumi yayin tafiya sai a rama cikin wasu kwanuka na dabam bayan wucewar Ramadana. 


Hadisan da za muyi amfani dasu anan sune :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


                      (1)


13170-  مُحَمَّدُ بْنُ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ بِإِسْنَادِهِ عَنْ مُعَاوِيَةَ بْنِ وَهْبٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فِي حَدِيثٍ قَالَ: هَذَا وَاحِدٌ إِذَا قَصَرْتَ أَفْطَرْتَ وَ إِذَا أَفْطَرْتَ قَصَرْتَ."


Daga Muhammad Bn Aliyu Bn Hussaini, da isnadinsa daga Mu'awiyata Bn Wahbin, daga Abu Abdullah (A. S) cikin Hadisi yace :


" WANNAN ABU 'DAYA NE, IDAN KAYI QASARU ZA KA SHA, KUMA IDAN KA SHA ZA KAYI QASARU. "


                         (2)


13171-  مُحَمَّدُ بْنُ الْحَسَنِ بِإِسْنَادِهِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيِّ بْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ عَلِيِّ بْنِ السِّنْدِيِّ عَنْ عُثْمَانَ بْنِ عِيسَى عَنْ سَمَاعَةَ قَالَ: قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع فِي حَدِيثٍ‏ وَ لَيْسَ يَفْتَرِقُ التَّقْصِيرُ وَ الْإِفْطَارُ فَمَنْ قَصَّرَ فَلْيُفْطِرْ."


Daga Muhammad Bn Hassan, da isnadinsa daga Muhammad Bn Aliyu Bn Mahbuub, daga Aliyu Bn Sindiyyi, daga Usmana Bn Isah, daga Sama'ata yace : Abu Abdullah (A. S) ya fada cikin Hadisi :


" BAI KASANCE ANA RABA (tsakanin) QASARU DA SHAN RUWA BA, DUK WANDA YAYI QASARU TO, YA SHA (ruwa cikin wannan hali). "


                          (3)


13172- الْفَضْلُ بْنُ الْحَسَنِ الطَّبْرِسِيُّ فِي مَجْمَعِ الْبَيَانِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: مَنْ سَافَرَ قَصَّرَ وَ أَفْطَرَ إِلَّا أَنْ يَكُونَ رَجُلًا سَفَرُهُ إِلَى صَيْدٍ أَوْ فِي مَعْصِيَةِ اللَّهِ."


Daga Fadhal Bn Hassan Ad-Dabariseey cikin Majma'ul-Bayaan, daga Abu Abdullah (A. S) yace :


" WANDA YAYI TAFIYA YAYI QASARU KUMA YA SHA RUWA, SAI DAI IN YA KASANCE MUTUMIN TAFIYAR TASA TA KASANCE FARAUTA KO KUMA CIKIN SABON ALLAH. "


- التهذيب 4- 328- 1021، و أورده بتمامه في الحديث 9 من الباب 5 من هذه الأبواب.


- مجمع البيان 1- 274، و أورده عن كتب أخرى في الحديث 3 من الباب 8 من أبواب صلاة المسافر.


Idan muka kalli wadannan riwayoyi za muga suna qara fassara ma'anar ayar da muke kawo ne a sama. 


MU ZAMA MASU YIN ADDINI KAMAR YADDA AKA UMARCE MU BA BISA RA'AYI KO BIN SON RAI BA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (23rd March, 2023/  1st Ramadan, 1444.H

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post