Sakon Wasikar Da Sarkin Kano Ya Aikawa Abba Kabir Yusuf zaɓaɓɓen Gwamanan Jihar Kano.Cikin wata wasiƙa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karɓi dimokradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmani shi ne yadda suka fito suka kaɗa kuri'unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ma'asumah  Nigeria News Update

 Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya Gwamna  Mai Ci Yanzu  Abba Kabir Yusuf Akan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris.


Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aiko da ta shi wasiƙar ta taya murna ga sabon Gwamnan Jihar Kano, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon.

Haka ma Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano.


A inda Shafin Bbc Ya Wallafa A Shafin Sa, Gamai Neman Karin Bayani zai iya bincikawa acan yagani.

Duka sarakunan sun miƙa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama'a da suka riƙa wayar da kan al'umma, aka yi zaɓe lafiya aka gama lafiya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post